Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Tallafin Bincike na Naira Biliyan 7.5 Ta Hannun TETFund

Gwamnatin Tarayya, ta hannun Hukumar Tallafa wa Manyan Makarantu ta Najeriya (TETFund), ta amince da bayar da tallafin bincike na kimanin naira biliyan 7.5 ga ayyukan bincike guda 174 da nufin ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire, haɓaka fitar da sakamakon bincike, da kuma bunƙasa ci gaba a manyan makarantun ƙasar.A cewar TETFund, adadin kuɗin tallafin da aka ware ga kowane aiki ya kai tsakanin naira miliyan 13.6 zuwa naira miliyan 49.97, inda aka mayar da hankali kan muhimman fannoni da suka kasance cikin abubuwan da ƙasa ta fi buƙata.

Waɗannan fannoni sun haɗa da kiwon lafiya da walwalar jama’a, noma, kimiyya da injiniya, wutar lantarki da makamashi, makamashi mai tsafta da wanda ake sabuntawa, da kuma fasahar tsaro da nazarin harkokin tsaro.

Hukumar ta bayyana cewa wannan tallafi wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati na inganta bincike da ƙirƙire-ƙirƙire domin samar da hanyoyin magance matsalolin ci gaba da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Post a Comment

Previous Post Next Post