Hukumar DSS Ta Saki Wani Mutum Da Ake Zargi Da Alaka Da Boko Haram Tare Da Biyan Sa Diyya

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta saki wani mutum mai suna Nura Idris bayan bincike ya tabbatar da cewa ba shi da alaƙa da ƙungiyar Boko Haram da ake zarginsa da ita.

Nura Idris

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, babban Daraktan DSS, Oluwatosin Adeola Ajayi, ne ya bayar da umarnin sakin Idris tare da amincewa a ba shi tallafin naira miliyan uku domin taimaka masa ya sake farfaɗo da rayuwarsa da harkokinsa.

Nura Idris, wanda manomi ne kuma makiyayi daga ƙaramar hukumar Soba ta jihar Kaduna, an kama shi ne a Suleja, jihar Neja, a shekarar 2024 bisa zargin alaƙa da ‘yan ta’adda kafin daga bisani a miƙa shi ga DSS.

Kwamitin binciken da DSS ta kafa ya gano cewa babu wata hujja da ke danganta shi da ayyukan ta’addanci, lamarin da ya sa aka ba da umarnin sakinsa nan take.

Idris ya yabawa shugabancin DSS bisa yadda aka kula da shi yayin da yake tsare, yana mai cewa kuɗin da aka ba shi za su taimaka masa wajen sake gina rayuwarsa.

Majiyoyin tsaro sun ce DSS na ci gaba da duba tsofaffin shari’o’in da suka shafi waɗanda aka tsare na dogon lokaci, domin tabbatar da cewa ba a ci gaba da tsare mutanen da ba su da laifi ba.

Rahotanni sun nuna cewa fiye da mutum 30 da aka sake duba shari’arsu sun amfana da diyya sama da naira miliyan 300, yayin da hukumar ke cewa matakin na nuna jajircewarta wajen kare haƙƙin ‘yan ƙasa tare da tabbatar da tsaron ƙasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post