Biyo bayan hare-haren sojojin da suka zo yaƙi da ta'addanci a ƙaramar hukumar Musawa da Matazu. Kachalla Maha ya sake bayyana da ƙarfinsa.
A baya idan ba ku manta ba, Kachalla Maha ya bayani tare da iƙirarin shi ne ya sace Birgediya Janar Rabe Abubakar mairitaya da matarsa a kan hanyarsu ta zuwa birnin Katsina.
Wanda daga baya ya yi bidiyonsa da matar suna bayyana buƙatunsa ga gwamnati. Jim kaɗan kuma bayan haka, sai kawai aka tsinci labarin ai Birgediya Janar Rabe Abubakar ya riga mu gidan gaskiya, yayin da kuma ita matar da sauran waɗanda Maha yake riƙe da su suna nan a hannunsu.
Bayan kwana biyu da faruwar wannan al'amari ne gwamnatin tarayya ta turo da bata koyar sojoji, inda shugaban rundunar sojojin Nijeriya Ya zo ya ƙaddamar da atisayen mai take Ofireshin Fansar Yamma.
Lallai kam sun ɗauki fansar, domin sun yi ƙoƙarin ceto matar mariga Rabe Abubakar tare da mutane huɗu (4) da suke a hannun Maha, duk da lokacin da sojoji suka samu matar, sun iske ta cikin jini tare da harbi a ƙafarta, wanda hakan ya tilasta aka hanzarta kai su asibiti domin kula da lafiyarta da sauran waɗanda aka kuɓutar.
Sai dai duk tsawon lokacin da Ofireshin ɗin ya ɗauka, bai iya kama Kachalla Maha ba duk kuwa da irin tsauraran dokokin da aka ɗauka da suka haɗa da: hana hawan babur da hana yin sana'ar POS da hana sana'ar caji, tare da ɗauke networks gabaɗaya a faɗin ƙananun hukumar Musawa da Matazu da Malumfashi da Kankia da Dutsinma na tsawon kwanaki 8.
A ranar Laraba bayan da aka buɗe network da kwana 5 sai ga labarin kisan babban taron Maha Mai suna Samagi ya bayyana a kafafen sada zumunta. Sai dai wannan ƙoƙarin na 'yan Sa Kai Ne ba na sojoji ba.
Wata majiya daga mazauna yankin sun tabbatar mini da cewa, lallai an bayyana cewa, mutanen garin Sayaya ne suka tona asirin shi Samagi da abokinsa waɗanda suka yi shigar burtu da nufin gudawa har 'yan sa kai suka kama shi suka hallaka shi.
Wai! Wannan ne dalilin da ya sa Kachalla Maha ya sake bayyana a ƙasar Sayaya inda ya hallaka mutane bakwai har lahira, ta hanyar yin harbin kan mai uwa da wabi.
A daren juya kuma, mun samu labarin bayyanarshi a garin Ɗanjanku ta lungu wadda ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Musawa, sai dai har ya zuwa yanzu da kike haɗa wannan rahoton ba mu samu labarin adadin ɓarnar da ya yi ba.