'Yansanda sun kama wani mutum mai suna Joe bayan an tsinci gawar budurwarsa a gidan da yake zaune a unguwar Ajidi Street, Edjeba, a birnin Warri na Jihar Delta.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 24 ga watan Yuni, 2026, lokacin da matar ta kai masa ziyara.
Daily Trust ta rawaito cewa masoyan sun shafe kwanaki suna zaune tare a gidan kafin rasuwar matar.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa an ga matar tana yawo cikin koshin lafiya a unguwar kwana guda kafin a tsinci gawarta.
Mazauna unguwar sun ce sun ji karar ihu daga gidan da safiyar Laraba, lamarin da ya sa mai gidan ya sanar da jami'an tsaro. Bayan isar 'yan sanda, sun tarar da gawar matar a cikin dakin wanda ake zargin.
An kama Joe, kuma an kai gawar matar dakin ajiye gawa domin gudanar da bincike da gwajin gano musabbabin mutuwarta.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Jihar Delta, Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai bayyana karin bayani ba.
