Gwamna Dauda Lawal Ya Amince da Biyan Alawus ga Masu Bautar Ƙasa a Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da biyan alawus ga mambobin shirin bautar ƙasa na NYSC da ke gudanar da hidimarsu a faɗin jihar.Amincewar na nuna ƙudirin gwamnatin jihar na ci gaba da inganta walwala da jin daɗin masu bautar ƙasar da ke ba da gudummawa wajen bunƙasa sassa daban-daban na ci gaban Jihar Zamfara.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Mahmud Muhammad Dantawasa, ya fitar, ya bayyana cewa amincewar ta shafi mambobin NYSC daga rukuni na Batch A Stream I da II har zuwa Batch C Stream I da II.

Post a Comment

Previous Post Next Post