Shugaban kwamitin tsaron ƙasa na majalisar dokokin Iran ya bayyana cewa tsarin kula da mashigar Hormuz tabbataccen abu ne ga Iran kuma mai dorewa da zai magance dukkan matsaloli.
Ɗan majalisar, Ebrahim Azizi, ya ce shirin ya ƙunshi dukkan fannoni da suka haɗa da dokokin zirga-zirga a yankin, tare da jaddada cewa Iran na ɗaukar matakai ne bisa muradun ƙasa cikin hikima da tsari.An shirya wannan tsari ne domin mayar da cikakken iko a hannun Iran kan mashigar Hormuz, musamman bayan ƙara tsanantar rikici da kuma matakan da ƙasar ta ɗauka wajen takaita zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.