IBADAN — Kungiyar Malaman Makarantu ta Kasa (NUT) reshen Jihar Oyo, ta umarci daukacin malaman makarantun firamare da na sakandare na gwamnati da ke jihar da su tsunduma cikin yajin aikin sai abin da ya turu, tun daga yau Litinin, 1 ga watan Yuni, 2026. Wannan mataki ya biyo bayan ci gaba da garkuwa da malamai da dalibai da ake yi a jihar.
Wannan umarni, wanda ya fito daga babban jagorancin kungiyar, na da manufar matsa lamba ga gwamnati domin ta dauki kwararan matakai na gaggawa wajen ceto wadanda aka yi garkuwa da su, wadanda ya zuwa yanzu ba a san inda suke ba.A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da Shugaban NUT na Jihar Oyo, Hassan Fatai, da Sakatarensa, Salami Olukayode suka sanya wa hannu, kungiyar ta bayyana cewa, tsawon lokacin da mutanen suka kwashe a tsare ya haifar da tsoro da fargaba a tsakanin malamai, sannan ya girgiza gwiwa da amincewar da ake da ita ga tsarin makarantun.
A cewar kungiyar, lamarin ya kuma sanyaya gwiwar iyaye wajen tura 'ya'yansu makaranta, tare da haifar da fargaba mai tsanani. Haka zalika, NUT ta jaddada cewa yajin aikin na da nufin jan hankalin mahukunta domin su tsananta bincike da kokari wajen ganin an saki malamai da daliban da aka sace ba tare da gadi ko guda ba.
Kungiyar ta yi kira ga daukacin malamai na fadin jihar da su bi wannan umarni dari bisa dari, su kasance masu bin doka da oda, sannan su tabbatar da tsaron lafiyarsu ta hanyar nisantar azuzuwan karatu a tsawon lokacin yajin aikin.
Daga karshe, kungiyar ta nuna juyayi da goyon bayanta ga wadanda aka yi garkuwa da su tare da iyalansu, tana mai jaddada cewa za ta ci gaba da tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa har sai an ceto dukkan mutanen lafiya kalau. Ta kuma sake jaddada aniyarta na kare walwala da tsaron malamai da dalibai a fadin kasa baki daya, inda ta bayyana cewa kariya ga al'ummar makarantu ita ce babban abin da ta sa a gaba.