Masu sharhin siyasa na Amurka, Cenk Uygur da Hasan Piker, sun bayyana cewa gwamnatin Birtaniya ta hana su shiga ƙasar saboda kalaman da suka yi na sukar Isra’ila da yaƙin Gaza.
Rahotanni sun nuna cewa hukumomin Birtaniya sun soke ko suka ƙi ba su izinin shiga ƙasar gabanin wasu taruka da aka shirya za su halarta a birnin London, ciki har da tarurrukan siyasa da na jami’o’i.
Cenk Uygur, wanda ya kafa shafin yada labaran siyasa na tyt.com, ya ce jami’an Birtaniya sun bayyana shi a matsayin “barazana ga zaman lafiyar jama’a” saboda wasu kalamai da ya yi wajen sukar manufofin Isra’ila da tasirin da ƙasar ke da shi a siyasar ƙasashen yamma.
Shi ma Hasan Piker ya ce an soke izinin shigarsa Birtaniya, yana mai zargin gwamnatocin yamma da tauye ‘yancin faɗin albarkacin baki kan batun Isra’ila da Gaza.
Har yanzu hukumomin Birtaniya ba su fitar da cikakkiyar sanarwa a hukumance ba kan lamarin, sai dai rahotanni sun ce akwai damuwa kan wasu kalamai da masu sharhin biyu suka yi a baya, waɗanda wasu ke ganin suna tayar da ƙiyayya ko rikici.
Wasu ƙungiyoyin Yahudawa a Birtaniya sun yi kira tun farko da a hana Hasan Piker shiga ƙasar, suna masu nuna damuwa kan wasu kalamansa da suka shafi Isra’ila, Hamas, da al’ummar Yahudawa.
Lamarin ya ƙara tayar da muhawara kan ‘yancin faɗar albarkacin baki, sukar Isra’ila, da iyakar ikon gwamnati wajen hana wasu fitattun mutane shiga ƙasa saboda ra’ayoyinsu na siyasa.