Babbar Kotun Kenya ta sami Ministan Lafiya, Aden Duale, da laifin raina kotu bayan gazawarsa wajen dakatar da aikin gina wata cibiyar killace masu kamuwa da cutar Ebola da Amurka ke tallafawa, duk da umarnin kotu da ya hana ci gaba da aikin.
Cibiyar da ake ginawa a sansanin sojin sama na Laikipia ta haddasa cece-kuce a Kenya. Masu suka sun ce an ƙaddamar da shirin ba tare da cikakken bayani ga jama'a ba, kuma suna zargin cewa tsarin zai iya jefa lafiyar 'yan Kenya cikin haɗari ta hanyar karɓar mutanen da suka yi hulɗa da cutar Ebola daga wasu ƙasashe.
Kungiyar Lauyoyin Kenya da Katiba Institute sun shigar da ƙara suna neman a dakatar da aikin, tare da zargin gwamnati da ci gaba da gina cibiyar duk da umarnin kotu. Kotun ta umarci gwamnati da ta bayyana yarjejeniyoyin da ta ƙulla da Amurka dangane da aikin.
Shugaban ƙasar Kenya, William Ruto, ya kare shirin, yana mai cewa yana daga cikin matakan shirye-shiryen tunkarar barkewar Ebola a yankin. Sai dai shirin ya haifar da zanga-zanga a sassan ƙasar, inda aka samu tashin hankali da asarar rayuka.
Kotun ta umarci Aden Duale da ya gurfana domin sauraron hukuncin da za a yanke masa kan laifin raina kotu, yayin da shari'ar kan makomar cibiyar Ebola ke ci gaba.