Kuskuren Da Yan Sandan Pakistan Suka Yi Ya Jawo Mutuwar Wata Yarinya Yar Australiya

 Wata yarinya ‘yar shekara tara ‘yar ƙasar Australia mai suna Hania Ahmed ta rasu bayan wasu jami’an ‘yan sanda a Pakistan sun buɗe wa motarsu wuta bisa kuskure, suna zaton motar ta wasu masu fashi ne.

Hania Ahmed

Lamarin ya faru ne a birnin Chakwal da ke lardin Punjab lokacin da iyalin Hania, waɗanda suka zo daga Perth domin ziyartar ‘yan uwa, suka fada hannun wasu ‘yan fashi masu makami. Yayin da ‘yan sanda ke mayar da martani ga fashin, wani jami’i ya yi kuskuren zaton cewa masu laifin suna tserewa ne da motar iyalin, lamarin da ya sa ya buɗe musu wuta. 

Harin ya yi sanadin mutuwar Hania nan take, yayin da mahaifinta da ɗan’uwanta suka samu raunuka kuma aka garzaya da su asibiti domin jinya. Mahaifiyarta kuwa ba ta ji rauni ba. 

Hukumomin ‘yan sandan Punjab sun amince cewa an samu kuskure a aikin jami’in, inda suka ce ya kauce wa ƙa’idojin amfani da ƙarfi. An dakatar da jami’in daga aiki, an kama shi, kuma an fara gudanar da bincike domin tabbatar da adalci. 

Firaministan Australia, Anthony Albanese, ya nemi a gudanar da bincike mai gaskiya da bayyana cikakkun bayanai game da lamarin, yayin da gwamnatin Australia ke ba iyalin tallafin ofishin jakadanci. 

Lamarin ya tayar da hankali a Pakistan da Australia, inda mutane da dama ke kira da a hukunta duk wanda aka samu da laifi tare da inganta hanyoyin aikin ‘yan sanda domin kauce wa sake afkuwar irin wannan mummunan kuskure a nan gaba. 

Post a Comment

Previous Post Next Post