Masallaci Mafi Tsufa A Kasar Burkina Faso

Masallaci shi ne wurin bauta da musulmai ke taruwa don yin sallah, musamman sallar Juma’a, da karatun Alkur’ani, da koyon addini. Masallaci yana da matsayi mai tsarki kuma shi ne gidan Allah a duniya. Ana gina shi da alamu kamar hasumiya (don yin kira ga sallah) da mihrab (wurin da limam yake tsayawa). Sallah a masallaci tana da lada fiye da sallah a gida, musamman idan aka yi ta da jama’a.

Masallaci

Masallacin Bobo-Dioulasso Masallaci ne a Bobo-Dioulasso, lardin Houet yankin Hauts-Bassins na kasar Burkina Faso.

A karshen karni na 19, yankin da masallacin yake a halin yanzu yana karkashin mulkin Masarautar Sia ne. A lokacin, masarautar ta na cikin haɗari, saboda ƙiyayya daga Masarautar Kénédougou. Tieba Traoré, sarkin masarautar Kénédougou, ya tara mayaka zuwa babban birnin Sia. Sarkin Sia ya tafi neman taimako don kare mulkinsa. Daga karshe ya gana da wani shugaban addinin Islama na yankin Almamy Sidiki Sanou wanda yace zai taimaka masa. A sakamakon haka, Sanou ya bukaci Sarkin Sia ya gina masallaci. An dakatar da harin Masarautar Kénédougou tayi kokarin dawowa da nisan kilomita 30 daga babban birnin kasar Sia, kuma daga karshe, an gina babban masallacin Bobo-Dioulasso.

An fara aikin ginin masallacin ne a shekara ta 1812, kuma an kammala shi a shekara ta 1832. Tun daga lokacin anyi yan gyare-gyare da dama a masallacin domin fadadawa da gyarawa. A cikin 1983, an yi rufin kwano don rufe wani ɓangare na farfajiyar masallacin. An gina masallacin ne da bulo na laka, da katako. Ya ƙunshi manyan hasumiya guda biyu.

Post a Comment

Previous Post Next Post