Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bayyana cewa matasan Kano ba kasalallu ba ne wajen kasuwanci , inda ya ce kawai su na bukatar tallafi ne domin bunƙasa kasuwancin su.
Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin ƙaddamar da shirin koyar da sana'o'i ga matasa da mata 150 da Hukumar Kula da Kimiyya da fasaha ta Ƙasa (NASENI) ta shirya a Kano.
Mataimakin Shugaban Ƙasar, wanda Musaddiq Mustapha Adam, Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Ababen More Rayuwa na Ƙananan Hukumomi daga Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ya wakilta, ya ce NASENI ta buɗe wa matasa ƙofar samun damar dogaro da kai.
Ya ce ya san irin ƙalubalen da matasa ke fuskanta a Kano wajen neman abin yi.
"Na san yadda rayuwa take ga matashin da ke ƙoƙarin kafa kansa. Na san abin da yake nufi idan ka ga takwarorinka suna ta fafutukar neman na yau da kullum ta hanyar ƙananan sana'o'i ko tukin babur mai ƙafa uku, suna jiran wata dama ta samu. Ba don kasala ba ne, sai dai saboda ba a buɗe musu ƙofar dama ba."
Shettima ya yabawa Shugaban Hukumar NASENI kuma Babban Darakta, Khalil Halilu, kan wannan shiri, yana mai cewa ya yi daidai da manufar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta Renewed Hope.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar NASENI, Khalil Halilu, ya ce manufar shirin ita ce bai wa matasa damar dogaro da kansu ta hanyar koyon sana'o'i.
Ya bayyana cewa wannan na ɗaya daga cikin shirye-shiryen da hukumar ta ƙaddamar domin ƙarfafa matasa.
Halilu ya ƙara da cewa shirin ya shafi fannoni daban-daban da suka haɗa da noma, kimiyya da fasaha, makamashi mai sabuntawa da sauran su.
Ya ce manufar ita ce a bai wa matasa, musamman mata, ƙwarewar da za ta ba su damar tsayawa da ƙafafunsu ba tare da dogaro da gwamnati kaɗai ba.
"Ba ma son mutane su ci gaba da dogaro da gwamnati kawai. Muna son mu ba su ƙwarewa da damar da za su yi tasiri a al'ummominsu, tare da tabbatar da cewa wannan ci gaba yana da ɗorewa," in ji Halilu.
