Sarkin Da Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Sama Da Miliyan Goma A Kasar Congo

Daga cikin Turawan da suka yi ta yunƙurin neman mulkar Afirka a ƙarshen karni na 19, Sarkin Belgium Leopold na biyu, za a iya cewa ya bar gado mafi girma kuma mafi ban tsoro.

Sarki Leopard

Yayin da manyan kasashen duniya ke fafatawa a wani yanki na daban, sarkin daya daga cikin Sarakuna a kasashen Turai ya yi nasa mulkin mallaka a cikin 100km2 na dajin Afirka ta tsakiya.

Ya yi iƙirarin cewa yana yin hakan ne domin ya kare ‘yan ƙasar daga bautarwa Larabawa, da kuma buɗe zuciyar Afirka ga Kiristocin mishan, da ƴan jari hujja na Yamma.

Azaba da fyade

Ya mayar da “Congo Free State” zuwa wani katafaren sansanin ‘yan kwadago, ya samawa kansa dukiya ta hanyar girbin roba da ya tilasta akan noma ya kuma ba da gudunmawa mai yawa wajen mutuwar mutane miliyan 10 da ba su ji ba ba su gani ba.

Abin da ake kira Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a har yanzu ba ta sake farfadowa ba.

Ya azabtar da kuma yi wa farar hular da ba su da makami fyade da yanke hannaye.

Sarki Leopold na biyu, ya musgunawa 'yan Kwango fiye da yadda ake zato. Ya dauki kasar a matsayin wani bangare na kadarorinsa, in da ya ke wadata kansa da arzikin albarkatun kasa da Allah ya huwace mata. Leopold dai bai san jinkai a Kwango ba lokacin da aka yi wa kasar mulkin mallaka.

Sarki Leopold ya jagoranci kasar Congo kamar kadarar sa tsakanin shekarar 1885 zuwa 1908 kafin daga bisani ta zama wani yanki da Belgium ta yiwa mulkin mallaka.

Post a Comment

Previous Post Next Post