TETFUND Ta Ƙarfafa Wa Masana Su Hanzarta Samar da Riga-kafin Cutar Lassa a Najeriya

Babban Sakataren Asusun Tallafa wa Ilimin Manyan Makarantu (TETFund), Dokta Sonny Echono, ya buƙaci masana kimiyya na Najeriya su ƙara ƙaimi wajen ƙirƙiro rigakafin cutar Lassa na farko da za a samar a ƙasar.

Echono ya yi wannan kira a ranar Litinin a Abuja yayin gabatar da sakamakon Babban Aikin Bincike kan Cutar Lassa da TETFund ta ɗauki nauyinsa, wanda Jami'ar Kimiyyar Lafiya ta Tarayya da ke Otukpo (FUHSO), Jihar Benue ta gudanar.

Ya bayyana cewa ci gaba da ɓullar cutar Lassa na zama babban ƙalubale ga lafiyar al'umma, yana mai jaddada cewa akwai buƙatar gaggawar amfani da binciken kimiyya wajen shawo kan matsalar.

Da yake mayar da martani kan sakamakon binciken, Echono ya ce abin da aka gano ya nuna cewa lokaci ya yi da Najeriya za ta wuce matakin binciken ilimi kawai, ta mayar da hankali kan samar da hanyoyin magance matsalolin da za su inganta rayuwar jama'a.

Ya ƙalubalanci masu binciken da su ba da fifiko wajen samar da rigakafin cutar, yana mai cewa allurar rigakafi ita ce hanya mafi inganci wajen dakile yaɗuwar cututtuka masu saurin kamuwa.

Shugaban TETFund ya kuma tabbatar wa masu binciken cewa asusun zai ci gaba da haɗa kai da hukumomin gwamnati domin tabbatar da cewa sakamakon binciken ya zama tushen aiwatar da tsare-tsaren inganta lafiyar jama'a.

A cewarsa, TETFund za ta miƙa sakamakon binciken ga cibiyoyi irin su Cibiyar Dakile da Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) da kuma Ma'aikatar Lafiya ta Tarayya, yana mai cewa idan aka tabbatar da ingancin binciken, hakan zai ƙarfafa yunƙurin kafa cibiyar bunƙasa rigakafi a Najeriya.

Echono ya yaba wa tawagar masu binciken bisa gudanar da binciken da zai taimaka wajen inganta tsarin kiwon lafiya, yana mai nuna fatan cewa ingantaccen kula da cututtuka irin su Lassa zai taimaka matuƙa wajen bunƙasa lafiyar al'umma a ƙasar.

Tun da farko, Mataimakin Shugaban Jami'ar FUHSO, Farfesa Francis Aba Uba, ya bayyana aikin a matsayin ɗaya daga cikin manyan ayyukan bincike mafi muhimmanci da jami'ar ta gudanar.

Ya tuna cewa kimanin shekara huɗu da suka gabata, TETFund ta bai wa jami'ar tallafin bincike na Naira miliyan 250 domin gudanar da bincike kan cutar Lassa, yana mai cewa wannan ya nuna amincewar da asusun ke da ita ga ƙwarewar masana kimiyyar Najeriya wajen samar da mafita ga manyan matsalolin lafiyar jama'a.

Uba ya ce ci gaba da barkewar cutar Lassa na ci gaba da jefa rayuka cikin haɗari, da cunkushe cibiyoyin kiwon lafiya tare da barazana ga tsaron lafiya a Najeriya da yankin Yammacin Afirka.

Ya gode wa TETFund bisa tallafa wa jami'ar duk da kasancewarta sabuwa, sannan ya roƙi gwamnatin tarayya da TETFund su ayyana FUHSO a matsayin Cibiyar Ƙasa ta Musamman Kan Binciken Cututtuka Masu Yaɗuwa.

Da yake gabatar da sakamakon binciken, jagoran tawagar masu binciken, Farfesa Joseph Okopi, ya ce Najeriya ce ke da mafi yawan masu kamuwa da cutar Lassa a duniya, inda ake kiyasin mutane tsakanin 5,000 zuwa 10,000 ke mutuwa sakamakon cutar a duk shekara.

Shi ma da yake gabatar da ɓangaren binciken na asibiti, Farfesa Audu Onyemocho, ya bayyana cewa an yi rajistar mahalarta binciken 1,266, yayin da aka binciki mutum 392 da ake zargin sun kamu da cutar Lassa a jihohin Benue da Kogi.

A cewarsa, zubar jini, tsufa da kamuwa da farfaɗiya sun kasance manyan abubuwan da suka fi haddasa mace-mace a tsakanin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar.

Da yake magana kan matakan bincike na gaba, tsohon Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) kuma mai ba tawagar binciken shawara, Farfesa John Idoko, ya ce babban buri shi ne samar da ingantaccen kuma amintaccen rigakafin cutar Lassa.

A wani ci gaba kuma, Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Kwamitin Kyaututtukan Ƙasa na Manyan Makarantu, wanda zai fara gudanar da sabon shirin ba da lambobin yabo ga fitattun masu bincike a fannin ilimi, tare da ware kyaututtuka na kusan Naira miliyan 365 a duk shekara.

Post a Comment

Previous Post Next Post