Shahararren Dan Damben Gargajiya Alh Yahaya Ibrahim Bargaja Ya Rasu

Allah SWT ya yiwa shahararren ɗan damben gargagajiyar nan, Alh. Yahaya Ibrahim Bargaja da aka fi sani da Bagobiri Ɗantcimau rasuwa.

Alh Yahaya Ibrahim Bargaja

Ya rasu ranar Litinin, 22/06 /2026 sanadiyar rashin lafiyar da yayi fama da ita a garinsu wato Bargaja dake Ƙaramar Hukumar Mulkin Isa ta Jihar Sakkwato.

Ɗan shekara 86 a duniya, Alh. Bagobiri Ɗantcimau ya yi shuhura a fagen damben gargagajiya musamman a ƙarshe ƙarshen shekarun 1960s zuwa 1970s da 1980s yadda har shahararren Makaɗin Damben ƙasar Hausa Marigayi Alhaji Muhammadu Bawa Ɗan'anace Yartsakkuwa, Gandi Sakkwato ya yi masa waƙa mai amshi "Yaƙi sabon Bagobiri, mai kayan hwaɗa".

A lokacin rayuwarsa ta dambe ya fafata da yan dambe irinsu Umaru Gundumi na Karime da Arnen Ɓalli da Audu Kure da Lawai Basafce da Maigari ba Imani da Ɗankincimi da Ado Ɗankore da Mushe da Gadede da Goto da Kundi da Shagon Wanke da sauran su.

Anyi jana'izarsa a garin nasu wato Bargaja kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Ya bar iyali da yan uwa da dama.

A cikin watan Afrilu na wannan shekara (2026) ya halarci bikin buɗe taron ƙasa akan tarihin rayuwa da waƙoƙin Makaɗa Muhammadu Bawa Ɗan'anace Yartsakkuwa, Gandi Sokoto da Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami'ar Usmanu Danfodiyo Sokoto ta shirya a birnin Sokoto tare da abokin fafatawarsa, wato Umaru Gundumi. 

Allah SWT ya jiƙan sa da rahama shi da sauran dukan magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani Alfarmar Sahibul Qiblataini Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam, amin ya rabbal alamin.

Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji), Jihar Zamfara, Nijeriya.

22/06 /2026.

Post a Comment

Previous Post Next Post