Shugaban kamfanin apple, Tim Cook, ya yi gargaɗin cewa ƙarin farashi a wasu kayayyaki da ayyukan kamfanin na iya zama abin da ba za a iya kauce masa ba yayin da buƙatar ƙirƙirarriyar basira (AI) ke ƙaruwa a duniya.
Cook ya bayyana cewa gagarumin saka hannun jari da ake yi wajen haɓaka fasahar AI, cibiyoyin adana bayanai, da sabbin kayan aikin kwamfuta na ƙara tsadar aiki ga manyan kamfanonin fasaha.
A cewarsa, yayin da kamfanoni ke fafatawa wajen samar da sabbin fasahohin AI, ana samun ƙarin buƙatar na’urori masu ƙarfi, kwakwalwan kwamfuta (chips), da makamashi, lamarin da ke ƙara kuɗin samar da kayayyaki da ayyuka.
Masana harkokin fasaha sun ce idan farashin ya ƙaru, hakan na iya shafar wasu kayayyakin Apple da suka haɗa da wayoyin iPhone, kwamfutocin Mac, da wasu ayyukan dijital da kamfanin ke samarwa.
Sai dai Cook ya jaddada cewa Apple za ta ci gaba da ƙoƙarin samar wa abokan cinikinta kayayyaki masu inganci tare da amfani da sabbin fasahohi ba tare da ɗora musu nauyi fiye da kima ba.
Masu sharhi kan harkokin kasuwanci sun ce wannan gargadi na nuna yadda bunƙasar AI ke sauya yanayin masana'antar fasaha, inda kamfanoni ke kashe kuɗaɗe masu yawa domin ci gaba da kasancewa a gaba a gasar fasaha.
Ana sa ran masu saka hannun jari da masu amfani da kayayyakin Apple za su ci gaba da sa ido kan yadda kamfanin zai daidaita tsakanin ƙarin kuɗin da yake kashewa kan AI da kuma farashin da yake ɗorawa kan kayayyakinsa.