"Ina Yaranmu suke? Kuma Yaushe Za Su Dawo? Tambayar da Dan Gwagwarmaya Verydarkman ya yi wa Gwamnan Jihar Oyo ke nan.
Daga Abubakar Shehu Dokoki
Jama'a wannan da kuke gani fitaccen ɗan gwagwarmaya ne a kudancin Najeriya wanda akewa laƙabi da Very dark man wato "VDM"
Tunda aka sace waɗannan ɗalibai guda Arba'in a jihar Oyo basu huta ba, mawaƙansu suna ƙira, 'yan gwagwarmayar su kuma suna zanga-zanga.
Hotunan da kuke gani, zanga-zangar shi wannan mutumin ya haɗa wacce Yakaisu har wajen gwamnan Oyo, wato seyi makinde, yana zuwa yakarɓi abin magana na makirfon yace masa "Ina ɗalibanmu? Kuma yaushe zasu dawo? Babu wanda ya harareshi bare har ayi yunƙurin kama wani daga cikin tawagarsa.
Gwamnan yana karɓar abin magana yace "Oyo is not chibok" I'm ready to sacrifice myself for Abducted children. Wato da Hausa cewa yayi "Ɗaliban Oyo ba kamar na Chibok bane" Na shirya sadaukar da rayuwata domin kuɓutar da yaran da akayi garkuwa dasu" wannan bayanin kamar anyi wa 'yan Arewa shaguɓe ne, amma dai kuma gaskiya ya faɗa wato "Oyo is not Chibok" ko munaso ko bamaso, su bazasu yarda ɗalibansu su daɗe kamar na Chibok ba.
Tunda suka saka neman ɗaliban nan a gaba, babu abinda ya kawar da hankalinsu, hatta maganar ministan tsaro, fadan rarara da Davido, babu ruwansu dashi, su kawai abu ɗaya suka saka agabansu "Kowa yana magana akan ɗaliban da aka sace" amma mu anan Arewa bayan kàshe janar Rabe Abubakar Saida akayi magana akan abubuwa wajen guda huɗu, Matan salim goje, zuwan rarara Abuja, faɗan rarara da Davido, dakuma sanya kakin soja akan maganar Ministan Tsaro.
Amma su shugabanninsu suna basu gudunmawa wajen buƙatar da take damunsu, kwanaki na karanta har yanzu akwai gwamnan da anan Arewa ya tsare wasu tun lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa data wuce.
Tabbas an bar mu a baya, sai dai Allah Ya gyara mana.
