Majalisar Wakilai ta Zimbabwe ta amince da wani ƙudirin gyaran kundin tsarin mulki da zai tsawaita wa’adin shugaban ƙasa daga shekaru biyar zuwa bakwai. Idan kudirin ya zama doka, zai iya bai wa Shugaba Emmerson Mnangagwa damar ci gaba da mulki har zuwa shekarar 2030.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan majalisa 216 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudirin, adadin da ya zarce rinjayen kashi biyu bisa uku da ake bukata domin gyaran kundin tsarin mulki. Yanzu kudirin zai wuce zuwa Majalisar Dattawa domin ci gaba da tantancewa.
Magoya bayan kudirin sun ce tsawaita wa’adin zai taimaka wajen samar da kwanciyar hankali a siyasa da kuma ba gwamnati damar aiwatar da shirye-shiryen ci gaba na dogon lokaci. Sai dai masu adawa da shi suna zargin cewa matakin wata hanya ce ta ƙara riƙe mulki da rage tasirin zaɓen jama’a.
Mnangagwa, mai shekaru 83, ya hau mulki ne a shekarar 2017 bayan kifar da tsohon shugaban ƙasa Robert Mugabe. Kudirin ya haifar da muhawara mai zafi a cikin Zimbabwe, inda wasu ke ganin zai ƙarfafa gwamnati yayin da wasu ke ganin zai iya raunana tsarin dimokuraɗiyya.
Masu sa ido kan siyasa sun ce sakamakon ƙarshe zai dogara ne da matakin da Majalisar Dattawa za ta ɗauka da kuma yiwuwar ƙalubalen shari’a da za su iya tasowa kan gyaran kundin tsarin mulkin.