Babban Hedikwatar Sojojin Najeriya ta bayyana cewa dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, wato Joint Task Force North West Operation FANSAN YAMMA (JTF NW OPFY), sun fara wani gagarumin farmaki mai suna Operation CLEAN SWEEP III, wanda ke nufin murƙushe ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ke addabar yankin Ƙaramar Hukumar Matazu da maƙwabtanta a Jihar Katsina.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA, Laftanar Kanal Aliyu Danua, ya fitar ga wakilan kafafen yaɗa labarai masu bibiyar harkokin tsaro a Abuja ranar Litinin.Sanarwar ta bayyana cewa an ƙaddamar da wannan farmaki ne bayan mummunan lamarin da ya yi sanadin rasuwar Manjo Janar mai ritaya Rabe Abubakar, wanda wasu da ake zargin ’yan ta’adda da ’yan bindiga ne suka yi garkuwa da shi tare da matarsa a yankin.
A cewar sanarwar, manufar wannan aiki ita ce gano da kuma kawar da waɗanda suka aikata wannan ta’asa, rusa hanyoyin sadarwa da sansanonin masu aikata laifuffuka, tare da dawo da zaman lafiya da tsaro a al’ummomin da abin ya shafa.
Tun bayan fara aikin a ranar Asabar, 14 ga Yunin 2026, dakarun sun gudanar da sintiri na yaƙi, farmaki bisa bayanan sirri, kewaye da bincike gida-gida, da kuma share maboyar masu laifi a wuraren da aka gano suna fakewa a yankin ayyukan rundunar.
Sanarwar ta ƙara da cewa dakarun sun samu gagarumar nasara a yankin tsaunukan Dikkawa da wasu ƙauyukan da ke kewaye da su.
Haka kuma, sojojin sun kai samame a maboyar ’yan ta’adda da aka gano a yankunan Adua, Nasarawa da Karaduwa, inda suka bincika tare da share sansanoni da wuraren da ake zargin masu aikata laifuffuka suna amfani da su.
Rundunar ta jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da wannan farmaki har sai an kamo ko an kawar da duk masu hannu a kisan marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar, tare da tabbatar da cikakken tsaro ga al’ummomin yankin.