Akwai wata irin baiwa ta musamman da sai a Najeriya kadai ake iya samunta. Wata siyasar hauka da ya kamata a yi saka a buhu da kwali, a fitar da ita zuwa wasu kasashen a matsayin albarkatun ƙasa.
Waɗannan mutane ba su iya biyan matasan N-Power hakkinsu ba.
Ba su iya cire tsofaffin ’yan sanda daga wutar azabar da ake kira PENCOM ba.
Ba su iya samar da aiki ba. Ba su iya kare rayukan mutane ba.
Amma da ikon kwaɗayi da addinin ɓarnar kuɗi, sun samu ƙarfin tunani don su ƙirƙiri ƙarin jihohi!
Mata da maza, ku shirya. Najeriya na shirin kara aure — ku gafarce ni, na ce aure — jihohi nake nufi!
Mataki na 1: Fassarar da Ma’anar “Ci gaban Ƙasa”
A cikin ƙamus na Najeriya, kalmar ci gaba ba ta nufin hanyoyi, makarantu, asibitoci, ko ayyuka. A’a.
Yanzu tana nufin sabbin letterhead, sabbin tambari, da sabbin alamar coat-of-arms wanda ɗan gwamna za a baiwa kwangilar bugawa.
Ba ka iya gyaran rufin aji, amma kana iya gina sabon ginin majalisa da tayal ɗin Italiya.
Ba ka iya biyan malamai, amma kana iya amincewa da “State Inauguration Gala” na naira biliyan biyu.
Mu dai muna kiransa “lalacewa a cikin tsari.”
Mataki na 2: Ninka Gazawa Cikin Hikima
Ƙirƙirar jihohi ba don warware matsaloli ba ne, don rarraba su ne.
Gwamna ɗaya azzalumi ya zama gwamnoni biyu azzalumai.
Majalisa ɗaya mai satar kuɗi ta zama majalisu uku masu ci gaba da cutar “budget.”
Kana da motocin jiniya na gwamnati biyu da ke toshe hanya? To masha Allah! yanzu za ka samu saba’in.
Wannan shi ake kira “democratic duplication of dysfunction.”
Mataki na 3: Girki da Yunwar Jama’a
Ka yi tunanin mutumin da ba ya iya ciyar da matarsa da ’ya’yansa biyu,
amma ya fito yana cewa zai ƙara aure mata biyu.
Ba saboda soyayya bane, a’a, saboda suna.
Yana tunanin idan yunwa ta ga kwanoni sun ƙaru, za ta girmama shi.
Wannan ne dabarar Najeriya:
Muna faɗaɗa talauci ne don ya yi kama da ci gaba.
Mataki na 4: Mu Manta da Gaskiya, Mu Rungumi Kwalliya
Hanyoyi na cike ramuka kullum mutuwa ake.
Makarantu sun zama gidajen tsuntsaye.
Asibitoci sun zama gidajen aljannu.
Malamai, sojoji, da ’yan sanda suna rayuwa kamar ’yan gudun hijira a ƙasarsu.
Rashin aikin yi ya fi ɗabi’ar kasar girma.
Amma kar ku damu — suna aiki tuƙuru…
suna zana sabbin taswira.
Saboda a cewarsu, sabbin iyaka suna warkar da tsohon wawanci.
Mataki na 5: Ƙara Kwamitoci Kan Kwamitoci
Maimakon biyan fanshon ’yan sanda, sai su sayi sabon mota mai tare harsashi (bulletproof) da wata mai jiniya (siren).
Maimakon gyaran rufin makarantu, sai su saka sabon labule a sabon ofis.
Maimakon gina masana’antu, sai su ƙirƙiri kwamitoci da ƙaramin kwamitin kula da babban kwamiti,
sannan su kafa kwamiti na musamman da zai “duba yadda ake kafa kwamiti.”
Yanzu muna da PA, SPA, SSA,
da SPA mai ɗaukar jakar PA.
Tsarin samar da aiki na Najeriya yana aiki — amma ba ga talaka ba.
Mataki na 6: Kwarewa a Yaudara da Sunan Mulki
Mulki a Najeriya tamkar Netflix series ne — labari ɗaya, kaka daban.
’Yan wasa suna sauyawa, amma rubutun ya nan: sata, murmushi, rantsuwa.
Sun ɗaura bukatar gwamnati a aljihun talaka,
sun mai da jama’a tukunyar miya ta ƙasa,
inda ’yan siyasa ke tsomawa duk lokacin da policy ta ji yunwa.
Kuma duk lokacin zaɓe, suna kiransa “democracy stew.”
Mataki na 7: Gina Rufin Zinare a Gidan mara gimshiki
Kafin ka raba jiha gida biyu, ka gyara rumbun abinci.
Kafin ka ƙara aure, ka ciyar da yaran da kake da su.
Kafin ka ƙara kujeru a majalisa, ka gyara kujerun makaranta da suka karye.
Amma a’a, suna nacewa su gina rufi na zinarea gidan da foundation dinsa ya fashe.
Zai dauki hankali kafin ya ruguje — amma fa yana da kyau a hotuna!
Gaskiyar Ƙarshe
Mu faɗi gaskiya karara:
Wannan ba mulki ba ne — wasa ne da hankali.
Ba gyara ba ne — maimaita lalaci ne.
Ba gina ƙasa ba ne — gina kai ne da dabarar kwashe kasafin kuɗi.
Kuma duk lokacin da suka sanar da sabuwar jiha, wani talaka a Najeriya zai ce:
“Ah, watakila wannan sabuwar jiha za ta kawo ci gaba.”
A’a, ɗan’uwana.
Zata kawo ƙarin motocin convoy mai siren, ƙarin sababbin labule, ƙarin kwamiti, da wata sabuwar waƙar yabo kafin su fara sata daga farko kamar yadda su ka saba. Saboda idan wannan hauka ya ci gaba, wata rana za mu farka mu tararbabu jama’a da za a mulka, sai jihohi ne kawai… suna mulkar aljannu.
