Ranar Wanka

Na zabi in sawa wannan rubutu suna ranar wanka ba a boyon cibi ganin yadda yakin aiki da kwakwalwa ya ta so Hausawa da Al'adunsu gaba. Kwanan nan gwamnatin tarayya ta samar da hadaddiyar manhajar karatu na bai daya wanda ciki aka samar da wasu darussa sababbi da na Cultural Creative Art da Nigerian History da kuma Islamic History.

Makaranta

Lallai sai Hausawa sun cire ganda da son kudi sun fito sun rubuta littattafai da za a rika koyar da yara wadannan darussa domin muddun muka yi kwance muka barsu su rubuta da kansu za a cakuda abubuwa kuma za a rubuta karya da za a dora yara masu tasowa a kanta.

Musamman a bangaren al'adun Hausawa saninmu ne wannan al'adar da muke kanta ba ita bace ta Bahaushe muna da tamu ta asali wadda mune muka santa in muka ki wallafa littattafai da kanmu tabbas zamu sha mamaki domin hatta rikicin makiyaya da manoma da tada zaune tsaye wata kila hadda sha da fataucin kwaya duk sai an hargitsa da sunan al'adun Hausawa.

Haka a bangaren sabon darasin Nigerian History nan ma abunda ya shafi arewacin Nigeria mune da kanmu ya dace mu yi rubutu in ba haka duk rikicin satar mutane da na boko haram da barayin shanu da sauransu sai an gani da sunan arewacin Nigeria.

Inda matsalar take a darasin Islamic History ta fi kamari domin ko mu din dama ana fama da danbarwa da banbancin ra 'ayi musamman a tarihin fiyayyen halitta da abunda ya shafi akida.

Lallai manyan malaman cikinmu da masu kudin cikinmu ya zama dole su karfafi gwiwar marubutanmu masu kudi suba da tallafi malamai su bada shawarwari sannan su yi editin.

Ya kamata yadda ake taimakon mawaka musamman na Hausa Hip -Hop a tallafi marubuta haka. Yau zaka ga mutum ya fara waka cikin Yan watanni ya shahara wannan yasa har yan yara shekara tara zaka gani cikin harkar amma a batun rubutu an barmu a baya ba mai taimakawa balle ya dau nauyi shiyasa mutanen mu suka watsar yau ga ranar abun ta zo.

Na yi alkawarin rubuta Littafi ''Al'adun Bahaushe Zalla'' Don makarantun sakandire. 

M. Aminu Musa

Post a Comment

Previous Post Next Post