Fitaccen malamin addinin Musulunci a Afirka, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya gode wa Shugaban Jamhuriyar Jama’ar Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune, bisa ba da cikakken tallafin karatu ga dalibai 140 ‘yan Najeriya domin yin karatu a jami’o’in ƙasar.
Tallafin, wanda ya haɗa da kuɗin makaranta da na rayuwa, ya biyo bayan roƙon da Sheikh ɗin ya gabatar ta gidauniyarsa, Sheikh Dahiru Usman Bauchi Foundation.A cikin wata wasiƙar godiya da ya sanya hannu, Sheikh Dahiru ya yabawa karamcin Shugaba Tebboune, yana mai cewa wannan mataki ya tabbatar da jajircewar Aljeriya wajen tallafa wa ilimi, haɗin kai, da kyawawan ɗabi’u.
Ya bayyana cewa Aljeriya ta daɗe tana zama abin koyi a Afirka saboda gaskiya da imani, ba saboda arziki ko ƙarfin iko ba.
A cewar daraktan ilimi na gidauniyar, Gwani Aliyu Dahiru Bauchi, dalibai 117 daga cikin 140 da suka samu tallafin sun kammala shirye-shiryen tafiya, yayin da saura 23 ke kan gyaran takardu kafin su tafi.
Masu cin gajiyar tallafin sun fito ne daga jihohin Bauchi, Gombe, Yobe, Kaduna, Taraba, Adamawa da wasu jihohi. Wannan shi ne rukuni na biyu da Sheikh Dahiru ya taimaka wajen samun tallafin karatu daga Aljeriya.