Daraktar Gudanarwa Ta MTN Foundation, Ta yi kira Ga matasan Najeriya Da Su Daina Mayar Da Hankali Kan Takardun Shaidar Karatu Kawai

Daraktar gudanarwa ta MTN Foundation, Misis Odunayo Sanya, ta yi kira ga matasan Najeriya da su daina mayar da hankali kan takardun shaida na karatu kawai, su kuma fara mai da hankali kan warware matsalolin da ke damun jama’a ta hanyar amfani da ƙwarewar da suka samu.

Ta bayyana hakan ne a yayin jawabinta na musamman a wani taron bita kan fasaha da kirkire-kirkire da aka gudanar a Legas kwanan nan. A yayin taron 2025 Data Science Nigeria Artificial Intelligence Bootcamp, Sanya ta kalubalanci matasan Najeriya da su yi amfani da iliminsu da ƙirƙirarsu wajen kawo sauyi mai ma’ana a cikin al’umma.

A cewarta, “Wasu mutane suna cewa suna da takardun shaidar karatu 50 ko 60. Amma ba yawan takardu ba ne abin da yake da muhimmanci; abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda kake amfani da abin da ka koya. A ƙarshe dai, tasirin abin da ka yi shi ne abin da ake kallo.”

Yayin da take jaddada alfanu da Najeriya ke da shi ta fuskar yawan matasa, Sanya ta nuna cewa Afirka ita ce nahiyar da ta fi kowacce yara, kuma Najeriya ita ce ƙasar da ta fi kowace matasa a duniya, wacce ke da matsakaicin shekarun jama’a 17 kacal. Duk da haka, ta shawarci mahalarta taron da su mai da hankalinsu wajen ƙirƙire-ƙirƙire da sana’o’in da za su magance matsalolin cikin gida.

Ta ce, “Da ƙwarewar da kuke da ita, to me ya biyo baya? Idan kuka zauna da ilimin kawai, ba zai amfanar da kowa ba. Dole ne ku gano matsalolin da kuke son warwarewa da kuma mutanen da kuke son taimakawa.”

A cewarta, nasara a yau tana nufin iya ƙirƙirar ƙima a kasuwa ta hanyar warware matsaloli da haɗin kai. Ta jaddada cewa fasaha dole ta kasance wadda ke mai da hankali kan ɗan Adam, tana mai cewa, “Abin da muke warwarewa don mutane ne, ba don injuna ba. Ko kai masanin bayanai ne ko injiniyan AI, aikin ka dole ne ya sanya fasaha ta zama mai amfani ga mutane, ta kawo ƙima ga rayuwarsu.

Post a Comment

Previous Post Next Post