Sojojin Najeriya Sun Ceto Matar Janar Rabe Wanda ya Rasu a Hannun Yanbindiga

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta ceto matar Janar Rabe Abubakar mai ritaya da ya rasu a hannun ƴan bindiga a jihar Katsina.

wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran rundunar Samaila Uba ya fitar, ya ce dakarunsu sun ceto Amina Abubakar bayan ɓarin wuta da ƴan bindiga, inda har ta kai ga ƴan bindigar sun harbi matar kafin su sake ta, su tsere cikin daji.

"Tana samun kulawa yanzu haka a asibitin sojoji, kuma tana samun sauƙi," in ji sanarwar.

Iyalan marigayin sun tabbatar wa BBC cewa sun samu labarin sakin mahaifiyar tasu wadda aka kama su tare.

Kamar yadda BBC ta hakaito daga ɗaya daga cikin ƴaƴansa, sun ce ba su yi ido biyu da ita ba amma an shaida musu cewa yanzu haka suna kan hanyar zuwa gida inda ake dakon isowarsu.

Sun ce sojoji ne suka taho da mahaifiyar tasu, inda suka buƙaci su shirya mata kayanta kafin su ƙarasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post