Tinubu ya Aika wa Majalisar Dattawa Kudirin kafa ƴan Sandan Jihohi a Najeriya

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya aika wa Majalisar Dattawa ƙudirin dokar gyaran kundin tsarin mulki da ke neman kafa ƴan sandan jihohi.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya sanar da hakan a zaman majalisar na ranar Talata, inda ya ce sanatocin za su fara duba ƙudirin a ranar Laraba.

Akpabio ya kuma bayyana cewa su ma gwamnatocin jihohi su yi nazarin ƙudirin.

Ƙudirin dokar na neman a yi gyare-gyare ga wasu sassan kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 domin samar da tsarin doka da zai ba da damar kafa rundunar ƴan sandan jihohi a faɗin ƙasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post