Tsohon Shugaban Sojin Sama Dikko Umar Zai Zama Sabon Sarkin Fulani A Jihar Kano

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, zai naɗa tsohon Hafsan Sojin Sama na ƙasa, Air Marshal mai ritaya Mohammad Dikko Umar, sarautar Sarkin Fulanin Ja’idanawa a ranar Juma’a mai zuwa.

Dikko Umar

Jaridar TheCable ta rawaito cewa, Sarkin ya sanar da naɗin Dikko Umar a watan Afrilu bayan rasuwar marigayi Alhaji Abubakar Buhari, wanda shi ne ya riƙe sarautar kafin rasuwarsa.

Sarautar Sarkin Fulanin Ja’idanawa na daga cikin manyan sarautun masarautar Kano da ke ƙarƙashin ikon Sarkin Kano. Majalisar masarautar ta ce an ba Dikko Umar sarautar ne domin karrama gudummawar da ya bayar wajen hidimar ƙasa.

An haifi Dikko Umar a ranar 20 ga Yunin 1955 a ƙaramar hukumar birni da ke jihar Kano. Ya shiga rundunar sojin saman Najeriya a watan Yulin 1976 a matsayin ɗalibin kwas na gajeren horo na 12.

Ya fara karatunsa ne a makarantar Victory College da ke Ma’adi a birnin Alƙahira na ƙasar Masar a shekarar 1963, kafin ya dawo Najeriya inda ya yi karatun sakandare a Sheikh Sabbah College da ke Kaduna, wadda daga baya aka sauya sunanta zuwa Sardauna Memorial College.

Dikko Umar ya fara aikin tukin jirgin sama a Benin a shekarar 1980 bayan samun horon soja da na matukin jirgi a Kaduna da kuma Birtaniya.

A shekarar 1983 an tura shi rundunar jiragen shugaban ƙasa, inda ya yi shekaru 16 daga cikin shekaru 23 da ya yi yana aiki a rundunar sojin sama.

An naɗa shi a matsayin Hafsan Sojin Sama na 17 na Najeriya a ranar 19 ga Satumbar 2010, mukamin da ya riƙe har zuwa ranar 3 ga Oktoban 2012.

Tsohon jami’in sojan ya kuma samu sarautu daban-daban a sassan ƙasar nan, ciki har da Olu Omo na Ipetu-Ijesa a jihar Osun, Oyukor Ovie a Delta, Okenwa Ana Amulu Oha na masarautar Nike a Enugu, da kuma Ja’idanawan Fika a jihar Yobe.

Post a Comment

Previous Post Next Post