Gwamnatin Venezuela ta yi kakkausar suka ga Trinidad da Tobago kan wani rikici da ya shafi zubewar mai a teku, wanda Venezuela ta ce yana barazana ga muhalli, kamun kifi, da al’ummomin da ke zaune a gaɓar tekunta.
Jami’an Venezuela sun bayyana cewa hotunan tauraron dan adam sun nuna cewa zubewar man ya samo asali ne daga yankin Trinidad da Tobago kafin ya bazu zuwa ruwan Venezuela. Sun kuma ce wannan zubewar ta fi girman wata makamanciyar matsala da aka samu a baya.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Venezuela ta bukaci Trinidad da Tobago da ta bayar da cikakken bayani kan lamarin, ta ɗauki matakan hana sake afkuwar irin wannan matsala, tare da magance illar da ta haifar wa muhalli.
Gwamnatin Venezuela ta kuma yi gargadin cewa za ta iya neman taimakon ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin bincike kan wanda ke da alhakin lamarin da kuma neman diyya idan ya zama dole.
A nata bangaren, Trinidad and Tobago ta ce ta tura jami’an tsaro na sama da na ruwa tare da jiragen sama marasa matuƙa domin binciken rahotannin da aka samu game da zubewar man.
Hukumomin ƙasar sun kuma nemi ƙarin bayanai daga Venezuela domin tabbatar da ainihin wurin da matsalar ta faru da kuma girman barnar da aka samu.
Masana muhalli sun yi gargadin cewa manyan zubewar mai na iya lalata albarkatun ruwa, gandun dajin mangrove, da wuraren kiwon halittun ruwa, tare da yin illa ga rayuwar mutanen da ke dogaro da kamun kifi da sauran harkokin ruwa.
Ana ci gaba da gudanar da bincike yayin da ƙasashen biyu ke ƙoƙarin tantance girman matsalar da tasirinta ga muhalli da tattalin arzikin yankin.