" Abarshi Allah shiyi
mai rahama,
Shi da Jibo amin ya
Allah,
Mun gode musu su
af farko,
Ka gadi gida ka ɗau
girma,
Kowah haihi kamatai
ya huta,
Ko gaba bai da hushi
ko ƙwara".
Inji Makaɗa Aliyu Ɗandawo Shuni ☝️a waƙarsa ta Marigayi mai martaba Sarkin Yauri, Abdullahi Jibril Abarshi mai amshi " Abdu bida maza ɗan Mamman, koma shirin daga ɗan Isah, na yanzu kay musu ko ta kwana, sai dai su bi ba don sun so ba".
Su wane ne Abarshi da Jibo da Makaɗa Aliyu Ɗandawo Shuni ya nemar ma rahama a wajen Allah SWT? Ya kuma nuna cewa Sarki Abdullahi Jibril Abarshi ya kai kamar su a ɗaukaka ya kuma gaji/gadi sauran nagartattun abubuwa daga wajen su?
Abdullahi Abarshi ya yi sarauta a Yauri daga shekarar 1890 zuwa 1904, Jibril(Jibo) ya gaje/gade shi daga shekarar 1904 zuwa shekarar 1915. Aliyu ɗan Abdullahi ya zama Sarki daga shekarar 1915 zuwa 1923 bayansa sai Abdullahi ɗan Jibril da aka yiwa wannan waƙar ya zama Sarki har zuwa wafatinsa a shekarar 1955.
Bayan rasuwarsa ne ɗansa Muhammad Tukur Abdullahi Jibril Abarshi ya gaje/gade shi a shekarar 1955 har zuwa shekarar 1981 da Allah ya karɓi abinsa.
Daga shekarar 1981 sai Alh. Shu'aibu Yakubu Abarshi ya zama Sarki har zuwa rasuwarsa a shekarar 1999 lokacin da aka naɗa Mai martaba Alh. Dakta Muhammad Zayyanu Abdullahi Jibril Abarshi CON (wato ɗa ga wanda aka yiwa wannan waƙa) wanda shi ne ke sarautar Yauri ya zuwa yau.
Abin lura anan shi ne Makaɗa Aliyu Ɗandawo Shuni ya ambaci Sarki Abarshi(Abdullahi Abarshi) da Sarki Jibril Abarshi (Jibo) domin ya bayyana sune suka assassa gidan sarautar da wanda yayiwa wannan waƙar wato Sarki Abdullahi Jibril (1923-1955) ya fito, wannan gidan sarautar ya samu tun a shekarar 1890 kuma ya zuwa yau daga cikin sa ne ake sarautar /Sarakuna a Yauri, kenan yau shekaru 136 kenan.
A wannan hoto Marigayi mai martaba Sarkin Yauri, Abdullahi Jibril ne.
Allah SWT ya jaddadawa dukan magabatanmu rahama tasa yasa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani Alfarmar Sayyadir Rahama Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam, amin ya rabbal alamin.
Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji), Jihar Zamfara, Nijeriya.
20/06/2026.
