A rana mai kamar ta yau 21 Ga Watan Yuni 2000 sama da mutane miliyan daya ne suka hallara a filin Idi da ke tsakiyar birnin Kano, domin shaida yadda aka kaddamar da shari'ar Musulunci a jihar da ta fi kowacce yawan jama'a a arewacin Najeriya.
A ranar 27 ga watan Oktoban shekarar 1999 tsohon gwamnan jihar Zamfara Ahmed Sani Yerima ya sanar da cewa jiharsa za ta fara aiki da shari'ar Musulunci. Wasu jihohin arewacin Najeriya guda 11 ciki har da Kano da Kaduna da ke da rinjayen Musulmi, sun bi sahu. Kiristoci sun yi zanga-zangar adawa da matakin kasancewar ba su san abin da zai biyo baya ba. Hakan ya janyo tashe-tashen hankula da salwantar rayukan dubbai jama'a.
Jihar Zamfara itace jiha ta farko da ta fara kaddamar da shari’ar musuluncin a ranar 27 ga watan Janairu na shekara ta 2000, sai jihar Kano dake biye mata baya inda gwamnan jihar na wancan lokaci Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya kaddamar da shari’ar a ranar 27 watan 6 na shekara ta 2000.
Jihar Sokoto da kuma jihar Katsina sun biyewa jihar Kano baya inda suma suka kaddamar da tsarin shari’ar musulunci a karshen shekarar ta 2000.
Jihohin Bauchi, Borno, Jigawa, Kebbi da kuma jihar Yobe suma sun bi sahun sauran jihohin da suka kaddamar da shari’ar tun da farko a shekarar 2001.
Su kuwa jihohin Kaduna, Niger da kuma jihar Gombe sun kaddamar da shari’ar musulunci ne a wasu sassa na jihohinsu da musulmai ke da rinjaye, kasancewar suna da al’umma da dama masu mabam-bamta addini a jihar.
Al’ummar musulmi dai sunyi farin ciki matuka da kaddamar da shari’ar a wancan lokaci.
Shari'ar Musulunci na da dadadden tarihi a arewacin Najeriya, domin tun gabanin mulkin mallakar Birtaniya a karni na 19 an yi amfani da shari'ar a daulolin Sakkwato da Borno da Kano da wasu birane, inda kuma ta yi tasiri saboda haka aka ga fa'idarta, kuma aka yi ta kira da dawo da tsarin na Shari'a bayan samun 'yancin kan Najeriya a 1960. Amma hakan ba ta samu ba sai a 1999 lokacin da Najeriya ta koma mulkin farar hula bayan shekaru gommai na mulki soji.
