Za a ba Iran Dala Biliyan 12 a Zango Biyu

Ministan harkokin tattalin arziki da kuɗi na Iran, Ali Madanizadeh, ya bayyana cewa za a saki dala biliyan 12 ga ƙasar a zango biyu bayan aiwatar da yarjejeniyar da ƙasar ta cimma da Amurka, inda za a fara sakin dala biliyan 6, sannan daga baya a sake sakin wani biliyan 6 kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.

Madanizadeh ya ce bisa sashe na 11 na takardar yarjejeniyar, Amurka ta ɗauki alƙawarin ba Iran cikakken damar amfani da kadarorinta da aka ƙwace ciki har da kuɗaɗen waje da aka tara.

Ministan ya kuma jaddada cewa waɗannan kuɗade na da alaƙa da kuɗaɗen man fetur na shekarun baya, kuma zancen cewa dole ne a kashe su ne wajen sayen kayayyakin Amurka kawai, jita-jita ce marar tushe, yana mai cewa za a ƙara fayyace yadda za a saki kuɗaɗen yayin tattaunawa.

Post a Comment

Previous Post Next Post