Ministocin harkokin wajen ƙasashen Pakistan da Turkiyya da Saudiyya da Masar sun buƙaci a samu yarjejeniya mai ɗorewa kuma tabbatacciya tsakanin Iran da Amurka.
A yayin wani taro da suka yi a birnin Alƙahira, ministocin sun kuma yi kira da a hanzarta cigaba a tattaunawar da ke gudana tsakanin ƙasashen biyu a Switzerland.A cikin sanarwar haɗin gwiwar da suka fitar, sun ce ya kamata a cimma matsaya wadda za ta kasance amintacciya, mai ɗorewa, kuma karɓaɓɓiya ga ɓangarorin biyu.
Sun ƙara da cewa dole ne yarjejeniyar ta yi la’akari da damuwar yankin, musamman batun tsaro da zaman lafiya a ƙasashen yankin Tekun Fasha.