Boko Haram sun kashe manoma 11 a Borno

AƘalla mutum 11 aka bayar da rahoton masu iƙirarin jihadi sun kashe a wasu ƙauyukan jihar Borno da ke arewacin Najeriya a ranar Asabar.

Wata ƙungiya mai yaƙi da masu iƙirarin jihadi a jihar Borno ta ce an kashe wasu manoma bakwai a yayin da suke shuka a gonakinsu.

Haka ma rahotonni sun ce an kashe wasu manoman huɗu a yankin tafkin Chadi.

Asusun bayar da lamuni na duniya ya yi gargaɗin cewa rikicin zai iya durƙusar da harkokin noma, lamarin da ka iya ƙara yaɗuwar talauci tsakanin al'umomin yankin.

Post a Comment

Previous Post Next Post