Alkali Ya Bi Ta Taga Ana Tsaka Da Shari'a Domin Tseratar Da Rayuwarsa

Wani alƙalin kotu ya bi ta tagar kotu bayan da ɓarayin daji suka yi yunƙurin ɗauke shi a garin Gwanki da ke ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina

Alƙalin ƙaramar kotun Shari'a mai suna Mohammed Muktar, ya tsallake rijiya da baya a ranar Laraba 30/07/2026 bayan da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka cika harabar kotun ɗauke da makamai a ƙauyen Gwarjo da ke ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina.

Al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 rana, inda rahotannin da jaridar Daily Trust ta wallafa suka ce maharan ɗauke da makamai sun shiga cikin harabar kotun, inda suka riƙa harbe-harbe domin tsoratarwa, sannan suka nemi a nuna musu inda alƙalin yake. Wanda ake kyautata zaton suna zo ne domin su kashe shi ko kuma su yi garkuwa da shi.

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar cewa Mohammed Muktar ya hango maharan tun daga nesa, lamarin da ya ba shi damar tserewa ta taga cikin gaggawa, tun kafin su ankara da abin da yake aikatawa, 'yan daƙiƙu kafin su isa cikin ɗakin shari'ar.

Wannan ya sabbaba tunanin, lallai wataƙila alƙalin yana da masaniyar shi suka zo nema, ko kuma wai abin nan da walaki goro cikin miya. Daga ƙarshe dai ɓarayin ba su samu damar tafiya da alƙalin ba sakamakon cika wando sa da iska da ya yi.

Post a Comment

Previous Post Next Post