Dakarun juyin juya halin musulunci na Iran (IRGC) sun yi ikirarin cewa sun lalata jiragen yaƙin Amurka kirar F-35 guda uku, tare da lalata wasu uku a wani hari da makamai masu linzami suka kai kan sansanin sojin sama na Al-Azraq da ke ƙasar Jordan kamar yadda BBC ta rawaito.
A wata sanarwa, IRGC ta ce harin martani ne ga hare-haren saman da Amurka ta kai kan gidaje biyu a tsibirin Qeshm, wanda ta ce ya yi sanadin mutuwar fararen hula uku, ciki har da wani yaro, yayin da wasu yara biyu suka jikkata.
Haka kuma, IRGC ta yi zargin cewa harin ya kashe wasu sojojin Amurka da ma’aikatan fasaha a rumfar gyaran jiragen yaƙi da ke sansanin, sai dai ba ta bayyana adadin waɗanda suka mutu ba.
Sai dai gwamnatin Amurka da ta Jordan ba su tabbatar da ikirarin Iran ba. A maimakon haka, sojojin Jordan sun ce tsarin kariyar sararin samaniyarsu ya tarwatsa makamai masu linzami guda biyar da aka harba daga Iran, kuma harin bai yi sanadin asarar rayuka ko wata babbar ɓarna ba.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata majiyar mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin Iran na lalata jiragen yaƙin F-35 ko kashe sojojin Amurka.
