An sanar da nadin tsohon mai horas da ƙungiyar Real Madrid Zinedine Zidane a matsayin sabon mai horas da tawagar ƙwallon ƙafa ta Faransa.
Didier Deschamps, kocin tawagar Faransa mafi daɗewa ya kammala aikin da ya kwashe shekara 14 yana yi a tawagar bayan cire Faransa da Spain ta yi a wasan kusa da ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta 2026.Zidane wanda ya taɓa lashe kofin duniya a matsayin ɗan wasan tawagar Faransa a shekarar 1998, ya kasance ba ya wani aiki tun bayan barin Real Madrid a karo na biyu a matsayin koci a shekarar 2021.
Zidane mai shekara 54 wanda ake kallo a matsayin ɗanwasan Faransa mafi bajinta, zai sanya hannu kan kwantaragin da zai ba shi damar jan ragamar ƙasar a wasannin neman gurbin gasar kofin duniya ta 2030.