Masu gabatar da ƙara a Albania na binciken wani ɗan kasuwa mai zama a birnin Miami, Artur Shehu, bisa zargin amfani da takardun mallakar ƙasa na bogi wajen sayar da wani yanki na gaɓar tekun Albania da aka ware domin gina katafaren wurin shakatawa na alfarma da ke da alaƙa da kamfanin saka hannun jari da Jared Kushner.
Masu bincike sun ce Shehu na fuskantar zarge-zargen safarar miyagun ƙwayoyi, halasta kuɗaɗen haram, da kuma mallakar filayen ta hanyar amfani da takardun bogi. Ana zargin cewa ya sayar da filin kan kusan Yuro miliyan 110 ga kamfanin da ke da alaƙa da aikin gina wurin shakatawar. Sai dai Shehu ya musanta dukkan zarge-zargen, yana mai cewa ya mallaki filin ne bisa doka kuma ya sayar da shi ta hanyar da ta dace.
Masu gabatar da ƙarar sun bayyana cewa ba su zargi Jared Kushner ko sauran masu saka hannun jari da aikata wani laifi ba, kuma babu wata shaida da ke nuna cewa sun san ana zargin takardun mallakar filin na bogi ne lokacin da aka sayi filin.
Shirin gina wurin shakatawar ya janyo zanga-zanga a Albania, inda mazauna yankin da masu kare muhalli ke cewa aikin zai lalata muhalli da kuma tauye haƙƙin masu ikirarin mallakar ƙasar. Zanga-zangar, wadda aka yi wa lakabi da "Flamingo Revolution", ta zama ɗaya daga cikin manyan zanga-zangar da aka yi a ƙasar cikin 'yan shekarun nan.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Manyan Laifuka ta Albania (SPAK) na ci gaba da binciken lamarin, yayin da kotu ta daskarar da wasu kadarori da kuɗaɗe da ake zargin suna da alaƙa da cinikin filin har sai an kammala bincike.