Hadarin Jirgin Ruwa a Kudancin Vietnam Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Masu Yawon Bude Ido Yan Indiya 15

 Aƙalla masu yawon buɗe ido ‘yan ƙasar Indiya 15 ne suka mutu bayan wani ƙaramin jirgin ruwa mai sauri (speedboat) ya kife a kusa da Tsibirin Phu Quoc da ke kudancin Vietnam, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

speedboat

An ce hatsarin ya faru ne yayin da jirgin ke dawowa daga yawon shakatawa a kusa da Tsibirin Hon May Rut Ngoai. Jirgin yana ɗauke da masu yawon buɗe ido ‘yan Indiya 32 da ma’aikatan jirgin ruwa 4 lokacin da ya kife sakamakon matsanancin yanayin teku.

Ƙungiyoyin ceto da suka haɗa da jami’an tsaron kan iyaka, sojojin ruwa da masu gadin bakin teku sun garzaya wurin domin gudanar da aikin ceto. Duk da matsalar yanayi, an samu nasarar ceto mutane 21, waɗanda aka kai wasu asibitoci domin samun kulawa ta gaggawa. Rahotanni sun ce wasu daga cikin waɗanda suka mutu sun makale ne a cikin jirgin bayan ya kife.

Firaministan Indiya Narendra Modi ya nuna alhini ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, tare da bayyana cewa jami’an ofishin jakadancin Indiya da ke Vietnam suna aiki tare da hukumomin ƙasar domin taimaka wa waɗanda suka tsira da kuma iyalan waɗanda lamarin ya shafa.

Rahotanni sun ce waɗanda suka mutu da waɗanda suka tsira ma’aikata ne na wata kamfanin wayar hannu mai zaman kanta a Indiya, waɗanda suka je Vietnam domin wani taron kamfani na shekara-shekara.

Hukumomin Vietnam sun fara bincike domin gano ainihin dalilin faruwar hatsarin. Sai dai rahotannin farko sun nuna cewa iska mai ƙarfi da manyan raƙuman ruwa na iya kasancewa daga cikin abubuwan da suka haddasa kifewar jirgin.

Tsibirin Phu Quoc na daga cikin wuraren yawon buɗe ido da suka fi shahara a Vietnam, inda mutane daga sassa daban-daban na duniya ke zuwa domin jin daɗin rairayin bakin teku da yawon shakatawa a tsibiran.

Post a Comment

Previous Post Next Post