Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa kan nasarar da jami'an tsaro suka samu wajen kubutar da dalibai da malamansu da aka sace a karamar hukumar Oriire da ke jihar Oyo bayan shafe kwanaki 56 suna hannun masu garkuwa.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai , Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya yabawa sojoji, DSS da 'yansanda saboda gudanar da aikin ceto ba tare da asarar rayuka daga bangaren wadanda aka sace ba.
Shugaban ya ce an kashe wasu daga cikin 'yan ta'addan da suka aikata laifin, yayin da aka kama mutum takwas, inda ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta tabbatar an hukunta masu hannu a kisan Mista Oyedokun da kuma sace daliban.
Rahotanni sun ce jami'an tsaro sun kashe akalla 'yan bindiga tara tare da kama takwas a farmakin hadin gwiwa da suka kai bisa bayanan sirri na DSS.
An sace akalla dalibai da malamai 45 ne bayan harin da 'yan bindiga suka kai makarantu uku a yankin Ogbomoso na karamar hukumar Oriire a ranar 15 ga Mayu, inda mutane biyu suka rasa rayukansu. Tinubu ya kuma umarci hukumomin agajin gaggawa da gwamnatin Oyo su samar wa wadanda aka ceto kulawar lafiya da tallafin gaggawa.
