AN GABATAR DA TARON SAURAREN KOKEN AL’UMMA NA SHIRIN CDP A JIKAMSHI WARD DOMIN SHIGAR DA BUKATU CIKIN BAJET DIN JIHAR KATSINA NA 2027
Taron jin koken al’umma na shirin Community Development Programme, CDP, ya gida a ne babban filin makarantar Pilot Primary da ke garin Jikamshi da ke ƙaramar hukumar Musawa. Manufar taron ita ce tattara buƙatun al’umma da aka gabatar a wurin a miƙa su ga mai girma Gwamnan jihar Katsina domin a saka su cikin kasafin kudin gwamnatin jihar Katsina na shekarar 2027.
A yayin taron, al’ummar Jikamshi sun mika saƙonnin godiya ga Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Dakta Dikko Umaru Radda, PhD, bisa irin ayyukan ci gaba da ayyukan alheri da gwamnatinsa ke aiwatarwa musamman a cikin garin Jikamshi da sauran sassan jihar.
Wakilin Akawunta Janar na Jihar Katsina, Malam Nura Tela, Wanda Alhaji Auwalu Shu’aibu Tela ya wakilta, shi ne ya gabatar da jawabin godiya a madadin al’umma. A cikin jawabinsa, ya lissafa wasu daga cikin ayyukan da gwamnatin ta cim ma wa a garin. Sannan ya yi kira da a ci gaba da bai wa mata fifiko a shirye-shiryen gwamnati, inda ya yaba da jajircewarsu da goyon bayan da suke ba wa Jam’iyyar APC.
A nasa jawabin, Alhaji Aminu Badaru Jikamshi ya bayyana wa al’umma tsarin yadda gwamnati ke tafiyar da ayyukanta. Ya tuna musu cewa, har yanzu muna cikin shekarar 2026, kuma akwai watanni shida da suka rage. Ya kara da cewa yana da yaƙinin cewa duk wata buƙata da al’ummar Jikamshi suka gabatar, Insha Allah za a samu nasarar cim ma ta.
Bayan ga nan, Farfesa Babangida Ladan shi ma ya bayyana jin daɗinsa gani da miƙa saƙon godiya ga mai girma Gwamnan jihar Katsina bisa ga manyan ayyukan da ya yi a wannan gari namu mai albarka. Sannan ya sake yin tuni ga mai girma akan ayyukan da suka nema a yi masu tun a waccan shekarar duk da kasancewar har yanzu akwai sauran lokaci, amma dai suna ƙara tuni.
Farfesan ya ƙara fito da buƙatun al'ummar ta garin Jiƙamshi, waɗanda ya ce: "Yana son a taimaka a gina masu dam na ruwa, domin al'ummar Jikamshi su amfana da yin noman rani, wanda za su riƙe kansu da shi. Ya kuma yi kira ga gwaman da a ƙara sama wa matasa da aikin yi, musamman ganin yadda Allah ya albarkacin garin da matasa 'yan boko.
Daga ƙarshe, ya sake yin kira da gwamnatin Malam Dikko Umar Radda da ya taimaka akwai wani babban kwalbati da yake nan a unguwar 'Yan Bita wanda ya kusa rushewa tun daga cikin har zuwa bakin titin. Farfesa ya yi kira da a taimaka a zo a gyara masu wannan kwalbati.
Shi dai wannan kwalbati yana nan a kusa da tsohuwar tasha, kuma kusa da tsohuwar kasuwa, babban kwalbati ne wanda ya ratsa ta cikin unguwanni. Kwalbati ya fara ne daga bakin titi har zuwa babban rafin garin, sai dai tun shekaru uku ko ma huɗu da suka shuɗe kwalbatin duk ya rufta yana ta zaizaye gefe, tare da rarake ƙasansa yana ƙara zurfi, wasu gidajen da ke kusa da shi ma, tuni ya wafci wani ɓangare daga gare su ya ƙara ma kansa. A taƙaice dai mutanen wannan unguwa suna cikin taraddadi musamman a duk lokacin da aka ce damuna ta dawo kai, don haka muke kira da a taimaka a gyara mana wannan kwalbati.
Daga gefe guda kuma, talakawa na ta tofa albarkacin bakinsu, musamman dangane da batun da ya shafi tsaron ƙaramar hukumar, inda wasu ke amfani da wani take (slogan): "Mu matsalar tsaro ta dame mu."
Taron ya haɗa manya da matsakaita da ma talakawan gari waɗanda suka haɗa da:
Mai martaba Alhaji Abdulƙadir Galadima, wakilin Hakimin Jikamshi, kuma mai garin Jikamshi, da Mai girma Tukur Ahmed Jikamshi, Wanda Alhaji Auwalu Badaru ya wakilta da Akawunta Janar na Jihar Katsina, Malam Nura Tela, Wanda Alhaji Auwalu Shu’aibu Tela ya wakilta da Alhaji Muntaƙa Ahmed Badaru (Barade), Wanda Alhaji Bishir Badaru ya wakilta da Alhaji Aminu Badaru Jikamshi, Sakataran Dindindin Na Ma'aikatar Kuɗin Jihar Katsina da Alh. Ibrahim Tukur Jikamshi, Shugaban Ma'aikatar Sanya Hannun Jari da Bunƙasa Kasuwanchi Na Jihar Katsina da Hon. Lawal H. Yaro, Dan Majalisar Jiha Mai Wakiltar ƙaramar hukumar Musawa, wanda S.A Yusuf Sani Ayiwasa ya wakilta da Hon. Abubakar Badaru Jikamshi, ɗan takarar Majalisar Jihar mai wakiltar ƙaramar hukumar Musawa da Ass Prof. Babangida Ladan Jikamshi da Hon. Haruna Magaji, Kansilan Jikamshi da Hon. Tukur Ɗahiru Jikamshi. Da sauran manyan-manyan jama'a da al'ummar gari.