Abubuwa Biyar da Ya Kamata Ka Sani Game da Haƙƙinka Idan 'Yan Sanda Sun Kama Ka

Haɗuwa da 'yan sanda na iya haifar da fargaba, musamman idan wanda aka kama bai san haƙƙoƙinsa da doka ta tanada ba. Saboda rashin sani, tsoro ko kuma bayanan da ba su dace ba, mutane da dama a Najeriya kan yi watsi da haƙƙoƙinsu lokacin kama su ko tsare su.

Sai dai kama mutum ba ya cire masa kariyar da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba shi. Sashe na 35(2) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) ya tanadi cewa duk wanda aka kama ko aka tsare yana da haƙƙin yin shiru, ko kuma ya amsa tambayoyi ne bayan ya tuntubi lauya ko wani mutum da ya zaɓa.

Ko da yake ya dace mutane su san kuma su nemi a mutunta haƙƙoƙinsu, ya kamata su guji yin fito-na-fito da jami'an tsaro. Kakakin 'yan sanda, DSP Ayanlade Olayinka, ya yi gargaɗin cewa yin turjiya ga kama mutum laifi ne, kuma duk wani ƙarfi da jami'an tsaro suka yi amfani da shi yayin kama mutum bai kamata ya kai ga duka ko cin zarafi ba.

Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya kuma tabbatar da wasu muhimman haƙƙoƙi ga wanda aka kama ko aka tsare, ciki har da haƙƙin rayuwa (Sashe na 33), 'yancin walwala (Sashe na 35), haƙƙin samun adalci a shari'a (Sashe na 36), haƙƙin sirri da rayuwar iyali (Sashe na 37), 'yancin faɗar albarkacin baki (Sashe na 39), da kuma 'yancin zirga-zirga (Sashe na 41).

Bugu da ƙari, Sashe na 35(4) ya tanadi cewa dole ne a gurfanar da wanda aka kama a gaban kotu cikin wa'adin da doka ta amince da shi.

Sanin waɗannan haƙƙoƙi na taimakawa wajen kare mutum daga kama ko tsare shi ba bisa ƙa'ida ba da kuma cin zarafi. Duk da haka, ana shawartar mutane su kasance masu natsuwa, su nemi taimakon lauya idan ya zama dole, kuma su nemi a bi su bisa tanadin doka.

Ga manyan haƙƙoƙi biyar da ya kamata kowa ya sani idan 'yan sanda ko wata hukumar tsaro ta kama shi:

1. Kana da haƙƙin sanin dalilin kama ka

A mafi yawan lokuta, jami'an tsaro sukan sanar da mutum dalilin da ya sa aka kama shi. DSP Olayinka ya ce wanda ake zargi yana da haƙƙin sanin dalilin kama shi, sai dai a wasu lokuta idan bayyana dalilin zai iya kawo cikas ga bincike ko gudanar da adalci.

Farfesa a fannin Dokar Kundin Tsarin Mulki, Nnamdi Aduba, ya ce mutum ya kamata ya lura da yanayin kama shi, wurin da aka kama shi da kuma ko jami'in na gudanar da aikinsa ne bisa doka. Sai dai ya ƙara da cewa idan an kama mutum yana aikata laifi kai tsaye, 'yan sanda na da ikon kama shi nan take.

2. Kana da haƙƙin yin shiru har sai ka tuntubi lauya

Doka ta ba wanda aka kama damar ƙin amsa tambayoyi ko bayar da bayani har sai ya tuntubi lauya. Aduba ya ce ya kamata 'yan sanda su sanar da mutum wannan haƙƙi kafin su ɗauki bayaninsa.

Haka kuma, DSP Olayinka ya bayyana cewa ya dace a karɓi bayanin wanda ake zargi a gaban lauya ko wani ɗan uwansa domin kare haƙƙoƙinsa.

3. Kana da haƙƙin samun lauya da sanar da iyalanka

Duk wanda aka kama yana da damar kiran lauya tare da sanar da wani daga cikin iyalansa inda yake. Wannan na tabbatar da cewa akwai wanda ya san inda aka tsare shi kuma zai iya taimaka masa wajen kare muradunsa.

Babban Lauya, Dakta Monday Ubani (SAN), ya kuma tabbatar da cewa wanda ake zargi yana da haƙƙin yin shiru har sai ya samu damar ganawa da lauya.

4. Ana ɗaukarka marar laifi har sai kotu ta tabbatar da laifinka

Kama mutum ko zarginsa da aikata laifi ba yana nufin ya aikata laifin ba. Kundin Tsarin Mulki ya tanadi cewa ana ɗaukar mutum marar laifi har sai kotu ta same shi da laifi.

Ubani ya ce dole ne a ba wanda ake zargi damar kare kansa, domin 'yan sanda ba za su iya zama masu zargi da kuma masu yanke hukunci a lokaci guda ba.

5. Kana da haƙƙin a bi da kai cikin mutunci da kuma tsare ka bisa doka

Kama mutum ba ya ba jami'an tsaro damar dukansa ko cin zarafinsa. Olayinka ya ce wanda aka kama yana da haƙƙin samun kulawar lafiya idan ya kamu da rashin lafiya, da kuma a tsare shi cikin yanayi mai kyau.

Ubani ya ƙara da cewa a mafi yawan lokuta wanda aka kama yana da damar samun beli daga 'yan sanda cikin sa'o'i 24, ko kuma cikin sa'o'i 48 idan babu kotu a kusa, gwargwadon tanadin doka.

Sai dai Farfesa Aduba ya shawarci jama'a da su kasance masu hikima da natsuwa yayin mu'amala da jami'an tsaro, musamman idan suna wuraren da babu jama'a, domin a aikace abubuwa na iya bambanta da yadda doka ta tanada.

Post a Comment

Previous Post Next Post