'Yan Sanda Sun Kwato Motar Hilux da Aka Sace, Sun Kama Mutane Biyu a Adamawa

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Adamawa ta kwato wata motar Toyota Hilux da aka sace tare da kama wasu mutane biyu da ake zargi da haɗa baki wajen aikata laifi da kuma karɓar kayan sata.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Suleiman Nguroje, ya fitar a ranar Alhamis.

Nguroje ya bayyana sunayen waɗanda aka kama da Mustapha Suleiman na unguwar Wuro Hausa da Rabiu Garba, mai shekaru 38, mazaunin Jambutu a Ƙaramar Hukumar Yola ta Arewa.

Ya ce an kama su ne bayan Aliyu Usman ya kai rahoto ga 'yan sanda cewa motar Toyota Hilux da ya saya kan kuɗi Naira miliyan 7.5 ta kasance mota ce da aka bayar da rahoton an sace.

Binciken farko ya nuna cewa an sace motar ne daga Jihar Rivers a watan Yunin 2026, sannan aka kai ta Jihar Adamawa ta hannun wani da ake kira Mati, wanda har yanzu yake tsere.

A cewar 'yan sanda, Mati ya haɗa baki da mutanen biyu da aka kama, inda suka sayar wa Aliyu Usman motar.

Da zarar Aliyu Usman ya gano cewa motar sata ce, sai ya garzaya ya sanar da 'yan sanda. Bayan samun rahoton, jami'an rundunar suka kama mutanen biyun, suka kwato motar, tare da gano ainihin mamallakinta.

Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Adamawa, Kabiru Hassan, ya yaba wa Aliyu Usman bisa gaskiya da haɗin kan da ya nuna, tare da jan hankalin jama'a da su tabbatar da sahihancin takardun mallaka da asalin kowace mota kafin su saya.

Ya kuma umarci jami'ansa da su ƙara ƙaimi wajen kamo Mati, wanda ya tsere, tare da tabbatar da cewa duk masu hannu a wannan laifi sun fuskanci hukunci.

Ya ƙara da cewa bincike na ci gaba, kuma da zarar an kammala shi za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.

A wani labari mai alaƙa, Rundunar 'Yan Sandan Jihar Oyo ta sanar da kama wasu mutum biyu da ake zargi da fashi da makami tare da ƙwato bindiga da ake zargin sun yi amfani da ita wajen kai hari a kan hanyar Oyo–Iwo Expressway a Ƙaramar Hukumar Afijio. Lamarin ya faru ne bayan samun kiran gaggawa cewa wasu 'yan fashi sun tare hanyar a kusa da ƙauyen Akoda a ranar 5 ga Yuli, 2026.

Post a Comment

Previous Post Next Post