A cikin talatainin dare, tawagar ƙasar Belgium ta kama ɗaya-ɗayar ƙasar da ta rage cikin 3 da suka karɓi baƙuncin wasan kofin duniya Amurika (USA) dukan Wa Na Kama (Ga mari ga tsinka jaka).
Belgium ta samu nasara a kan Amurika da ci 4 da 1 a cikin mintina 90 da suka gwabza, wannan ita ce nasara ma fi girma da wata ƙungiya ta samu a Zagayen 'yan 32.
Idan ba ku manta ba, a shekaran juya ne, shugaba Donald Trump ya fitittike akan dole sai an janye jan katin da aka ba wa ɗan wasansa Balogun, sai dai Belgium sun ce ba komai, duk da Balogun a cikin wasan suka nannaga masu ruwan ƙwallaye har 4 a raga.