Faransa Da Sifaniya, Kafa Wani Tarihin Ko Daukar Fansa?

Gobe Talata da misalin ƙarfe 8 na dare za a sake fafatawa tsakanin tawagar ƙasar Faransa da ta Sifaniya (Spain) a wasan dab da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya da ake gabatarwa a ƙasashen Amurika da Canada da kuma Mexico, wanda idan har Faransa ta samu rinjaye a kan ƙungiyar ta Sifaniya zai zama karo na uku a jere da take zuwa wasan zagayen ƙarshe na gasar ta cin kofin duniya, idan za mu iya tunawa, a gasar da aka yi wadda ta wuce ta shekarar 2022 wadda ƙasar Qatar ta karɓi baƙunci, nan Faransa ce ta fafata da ƙasar Argentina wanda wasan ya kai su bugun daga kai sai mai tsaron taga, bayan da wasan ya tashi 3 da 3. 

Faransa da Sifaniya sun taɓa karawa a gasar cin kofin duniya (World Cup), mafi shahara kuma babban wasan da suka yi shi ne a gasa ta shekarar 2006 wanda ƙasar Germany ta karɓi baƙunci, a matakin zagaye na ‘yan ƙungiyoyi 16 (Round of 16). A wannan wasan, Faransa ta lallasa Sifaniya da ci 3-1, inda aka zura ƙwallayen ta hannun Franck Ribéry da Patrick Vieira, da kuma Zinedine Zidane, bayan da Sifaniya ta fara zura ƙwallo ta hannun David Villa.

​Haka nan, sun taɓa yin kunnen doki 1-1 a matakin rukuni a gasar cin kofin duniya a shekarar 1982 wanda ƙasar Sifaniya ta karɓi baƙuncin wasan.

Lallai wasan gobe akwai kallo. A ganinku wane ne zai fi haskawa a wasan na gobe?

Post a Comment

Previous Post Next Post