Da safiyar yau Litinin 13/07/2026, mun samu rahoton ɓullar ɓarayin daji masu garkuwa da mutane zuwa garin Ɗankado da yake nan bayan garin Sabon Layi da ke ƙaramar hukumar Musawa. Wannan shi ne kusan karo na uku da suke zuwa garin suna ɓarna.
Sai dai a wannan zuwan, ɓarayin sun yi nasarar harbin wani mutum mai suna Mansur, sai kuma wasu mutane biyu Ƙasimu da Jamilu da suka iske a gona suna aiki suka kashe su nan take.
An garzaya da Mansur asibiti domin duba lafiyarshi, su kuma Jamilu da Ƙasimu muna addu'ar Allah ya gafarta masu.
Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya ɗauki alhakin kai harin, sai dai ana zargin ko dai yaran Kachalla Muhammadu ne da yake da iko da dazukan Matazu ko kuma Wada wanda yake kula da dazukan Musawa, sai dai an fi ƙarfafa zargi ga shi Wada ɗin.