Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ta gabatar da wani sabon shirin tallafi da zai bai wa kowace daga cikin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasashe 211 da ke ƙarƙashinta, ciki har da Hukumar Kwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF), damar samun har zuwa dala miliyan 20 domin bunƙasa harkokin ƙwallon ƙafa.
A cikin sanarwar da FIFA ta fitar a ranar Talata, ta ce shirin ya ƙunshi wani zaɓaɓɓen tallafi na sau ɗaya na dala miliyan 20 ta hanyar sabon FIFA Fast Forward Programme (FFFP) domin aiwatar da manyan ayyuka na musamman, tare da ƙara yawan kuɗaɗen tallafin ci gaban ƙwallon ƙafa da ake bayarwa ƙarƙashin shirin FIFA Forward.
Bisa ga sabon tsarin, kowace ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasa za ta karɓi dala miliyan 20 a tsakanin shekarun 2027 zuwa 2030, maimakon dala miliyan 8 da ake warewa a halin yanzu.
Za a ƙara wannan tallafi zuwa dala miliyan 22 ga kowace ƙungiya tsakanin shekarun 2031 zuwa 2034, sannan ya kai dala miliyan 24 daga shekarun 2035 zuwa 2038.
Sai dai a madadin wannan ƙarin tallafi, FIFA za ta ci gaba da riƙe cikakken ikon tafiyar da sabon kamfanin FIFA Forward Enterprise (FFE), tare da kasancewa ita kaɗai ke da ikon yanke hukunci kan mulkin ƙwallon ƙafa, shirya gasa, jadawalin wasanni da sauran dokoki da ƙa'idojin wasan.
Haka kuma, a ƙarƙashin shirin, FIFA za ta sayar da wani ƙaramin kaso na hannun jarinta a harkokin kasuwancinta ga masu zuba jari masu zaman kansu, matakin da ya jawo suka daga wasu ɓangarori, musamman Hukumar Kwallon Ƙafa ta Turai (UEFA).
Sai dai FIFA ta bayyana cewa ƙarin kuɗaɗen za su taimaka wajen gina da inganta filayen wasa, horar da masu horaswa, tallafa wa ƙungiyoyin ƙasa, shirya gasa, bunƙasa ƙwallon ƙafa na matasa da kuma ƙwallon ƙafar mata.
Sanarwar ta ce, idan aka amince da shirin, dukkan ƙungiyoyin membobin FIFA za su amfana da:
- Tallafin gaggawa na zaɓi na dala miliyan 20 ga kowace ƙungiya domin ayyuka na musamman ta hanyar FFFP.
- Dala miliyan 20 ga kowace ƙungiya a ƙarƙashin FIFA Forward tsakanin shekarun 2027 zuwa 2030.
- Dala miliyan 22 tsakanin shekarun 2031 zuwa 2034.
- Dala miliyan 24 tsakanin shekarun 2035 zuwa 2038.
FIFA ta bayyana cewa za a samar da wannan kuɗi ne ta hannun FIFA Forward Enterprise (FFE), wani sabon kamfani mallakin FIFA wanda zai haɗa dukkan harkokin kasuwanci da shirya manyan wasanninta. Hukumar ta ce za ta ci gaba da riƙe cikakken iko a kan kamfanin, yayin da za ta tara har zuwa dala biliyan 4.2 daga masu zuba jari na dogon lokaci bisa kimar farko ta dala biliyan 20.
Hukumar ta kuma tabbatar da cewa duk ribar da kamfanin FFE zai samu za a sake mayar da ita wajen bunƙasa ƙwallon ƙafa a faɗin duniya.
Shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya ce manufar wannan shiri ita ce tabbatar da cewa ci gaban kasuwancin ƙwallon ƙafa yana amfani ga dukkan ƙasashen da ke ƙarƙashin FIFA.
Ya ce, "Ƙwallon ƙafa shi ne wasa mafi shahara a duniya, kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban al'umma. Wasu ɓangarori na wasan sun samar da dimbin kuɗaɗen shiga, kuma muna maraba da hakan saboda yana taimaka wa wasan gaba ɗaya. Amma aikinmu shi ne tabbatar da cewa sauran sassan ƙwallon ƙafa ma sun ci gajiyar wannan ci gaba. FIFA tana nan ne domin tallafa wa ci gaba mai ɗorewa da haɗin kai a kowane lungu na duniya."
Infantino ya ƙara da cewa kowace ƙungiyar memba ta FIFA ya kamata ta samu damar cin gajiyar wannan tallafi domin tsara makomarta da kanta ba tare da dogaro da wasu ba.
Ya ce, "Kowace ƙungiyar memba ta FIFA ya kamata ta sami damar samun rabon da ya dace na wannan tallafi domin tsara makomarta da kanta. Wannan wani mataki ne na tabbatar da adalci da daidaito wajen bunƙasa ƙwallon ƙafa a faɗin duniya."
FIFA ta ce sabon tsarin zai fara aiki ne kawai idan mafi rinjayen ƙungiyoyin membobinta da kuma Majalisar FIFA sun amince da shi, kamar yadda dokokin tafiyar da hukumar suka tanada.
Hukumar ta ƙara da cewa idan aka amince da wannan shiri, jimillar kuɗaɗen da za ta ware domin bunƙasa ƙwallon ƙafa a cikin shekaru huɗu masu zuwa za su haura dala biliyan 10, wanda zai zama mafi girman tallafin ci gaban wasanni da wata hukuma ta taɓa warewa.
A cewar FIFA, wannan shiri ya biyo bayan nasarorin da aka samu daga gasar Kofin Duniya ta FIFA ta 2026, inda ƙarin tallafin ci gaban ƙwallon ƙafa ya taimaka wa ƙasashe irin su Cabo Verde da Curaçao samun tikitin shiga gasar Kofin Duniya karo na farko.
Hukumar ta kuma bayyana cewa FIFA Fast Forward Programme zai ba ƙungiyoyin membobinta damar samun ƙarin jari domin aiwatar da manyan ayyuka na dogon lokaci, ciki har da gina filayen wasa, cibiyoyin horas da 'yan wasa na ƙasa da sauran muhimman gine-ginen ci gaban ƙwallon ƙafa.