Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa ɗarikar Tijjaniyya kan shirya addu'a ta musamman domin neman zaman lafiya mai ɗorewa da bunƙasar tattalin arzikin Najeriya.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar.
Gwamna Yusuf ya yi wannan yabo ne bayan kammala taron zikiri na shekara-shekara da addu'o'i na musamman ga Najeriya, wanda aka gudanar a Fadar Sarkin Kano a ranar Juma'a.
Ya bayyana cewa addu'ar ta zo a kan lokaci, yana mai cewa shugabanni a kowane mataki na buƙatar shiriya daga Allah domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma tare da aiwatar da ayyukan ci gaba masu amfani ga jama'a.
Da yake jawabi ga dubban mahalarta taron, gwamnan ya ce ya sanar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu game da taron addu'ar, kuma shugaban ya nuna farin cikinsa da wannan shiri. Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya yi niyyar halartar taron da kansa, amma wani gaggawar aiki ya hana shi.
Gwamna Yusuf ya tabbatar wa masu shirya taron cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da ba da goyon baya ga irin waɗannan tarukan addini a nan gaba.
Har ila yau, ya gode wa iyalan Sheikh Ibrahim Nyass da suka zo daga ƙasar Senegal domin halartar taron, tare da sauran manyan malamai daga sassa daban-daban na Najeriya.
A nasa jawabin, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya tabbatar wa Gwamna Yusuf da cikakken goyon bayan ɗarikar Tijjaniyya tare da ci gaba da yi masa addu'ar samun nasara a mulkinsa.
Sarkin ya ce mambobin ɗarikar suna yi wa Gwamna Yusuf addu'a tun daga shekarar 2022, kuma za su ci gaba da hakan saboda ƙoƙarinsa wajen bunƙasa Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.
Addu'ar ta ɗauki fiye da sa'o'i shida kafin a kammala ta da addu'o'in zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.
