Gwamnati Ta Raunana 'Yan Sanda Da Gangan, Ta Ƙara Tsananta Rashin Tsaro — Okiro

Tsohon Sufeto Janar na 'Yan Sandan Nijeriya, Mike Okiro (mai ritaya), ya zargi Gwamnatin Tarayya da raunana Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya ta hanyar ƙin samar mata da isassun makamai da kayan aiki, yana mai cewa hakan ne ya taimaka wajen ta'azzarar matsalar rashin tsaro a ƙasar.

Okiro ya bayyana hakan ne a ranar Ta ilata yayin taron First Daily Na tional Dialogue on Security da aka gudanar a Abuja.

Ya ce rundunar 'yan sanda ita ce babbar hukuma mai kula da tsaron cikin gida, amma gazawar gwamnati wajen samar mata da makamai da sauran kayan aiki ya rage mata ƙarfin yaƙi da aikata laifuka.

"A ganina, gwamnati ita kanta tana taimakawa wajen ƙara rashin tsaro.

"'Yan sanda su ne jagororin kula da tsaron cikin gida. Amma gwamnati da gangan, ba tare da tsoron a musanta ni ba, ta kwace musu ƙarfi ta hanyar rashin ba su makamai. Sakamakon haka shi ne rashin tsaro," in ji shi.

Ya ƙara da cewa a yanzu 'yan sanda na fuskantar ƙungiyoyin masu aikata laifuka da suka mallaki manyan makamai, alhali su ba su da kayan aikin da suka dace domin sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora musu.

"Lokacin da ɗan sanda zai riƙa sintiri da sanda kawai ya wuce. Yanzu gwamnati dole ta samar wa hukumomin tsaro da makamai, na'urorin sadarwa, motocin sulke da sauran kayan aikin gudanar da aiki."

Okiro ya kuma ɗora alhakin ƙarancin jami'an 'yan sanda kan gazawar gwamnati wajen ɗaukar sabbin ma'aikata domin maye gurbin waɗanda suka yi ritaya, suka rasu ko suka bar aiki.

Ya tuna cewa lokacin da yake Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan 'Yan Sanda (Police Service Commission) a shekarar 2013, an gano cewa ba a ɗauki sabbin jami'ai ba tsawon shekaru biyar, duk da cewa rundunar ta rasa jami'ai 59,730 sakamakon ritaya, mutuwa da wasu dalilai.

"Mun gano cewa tsawon shekara biyar ba a ɗauki sabon ɗan sanda ko guda ba. Duk da haka akwai dubban matasa 'yan Nijeriya masu digiri da ba su da aikin yi."

Har ila yau, ya soki rashin haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, yana mai cewa jinkirin musayar bayanan sirri saboda tsarin ofisoshi na hana ɗaukar matakin gaggawa.

"Lokacin da nake Sufeto Janar, na rubuta wa Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro cewa dole hukumomin tsaro su riƙa aiki tare. Idan Daraktan DSS na Mubi ya samu bayanai, ya kamata ya sanar da DPO nan take maimakon aika rahoto zuwa Abuja kafin a ɗauki mataki. A wannan lokacin masu laifi ba za su jira ba."

A nasa jawabin, tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya bayyana damuwa kan yadda ake kashe kuɗaɗen tsaro a ƙasar.

Ya ce fiye da kashi 75 cikin 100 na kasafin kuɗin tsaro na Nijeriya na tafiya ne wajen biyan albashin ma'aikata, lamarin da ke barin ƙarancin kuɗi don sayen makamai, gyaran kayan aiki da kuma sabunta ƙarfin rundunonin soji.

"Fiye da kashi uku cikin huɗu na kasafin kuɗin tsaron Nijeriya na tafiya ne wajen biyan ma'aikata kawai. Wannan ya bar ƙaramin kaso don sayen kayan aiki, kula da su da kuma sabunta su.

"Bugu da ƙari, jimillar kuɗin da Nijeriya ke kashewa a harkokin soja bai kai kashi ɗaya cikin ɗari na GDP ba. Ga ƙasar da ke fama da matsanancin rashin tsaro, wannan ya kamata ya zama abin dubawa."

Irabor ya kuma bayyana cewa bayanan Open Treasury Portal na Ofishin Akanta Janar na Tarayya sun nuna cewa kuɗaɗen da ake fitarwa domin ayyukan soji sun yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da abin da aka amince da shi.

A cewarsa, an ware ₦20.56 biliyan domin sayen kayan aikin rundunar sojin ƙasa a kasafin shekarar 2025, amma zuwa yanzu an saki kashi 7.1 cikin 100 kacal, wato ₦1.46 biliyan.

Post a Comment

Previous Post Next Post