Kwamitin da Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa domin sake duba sakamakon tantance ma’aikatan ƙananan hukumomi ya fara aikin tantance ma’aikatan da abin ya shafa kai tsaye.
An fara aikin ne a ranar Litinin, 27 ga Yuli, 2026, inda aka tantance ma’aikata 100 daga ƙananan hukumomin Kaita, Batagarawa da Katsina.
Daga cikin ma’aikatan 100, Kaita na da 10, Batagarawa 29, yayin da Katsina ke da 61.
Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Mai Ba Gwamna Shawara kan Binciken Ƙananan Hukumomi, Hon. Lawal Rufa’i Safana, ya gudanar da aikin ne bayan kammala nazarin korafe-korafe kusan 900 da ma’aikatan da abin ya shafa suka gabatar.
An ce manufar tantancewar ita ce tabbatar da sahihancin korafe-korafen, domin a biya ma’aikatan da aka tabbatar da cancantarsu albashinsu na wata-wata, ciki har da basussukan albashin da suka tara.
A baya, Gwamnatin Jihar Katsina ta gudanar da aikin tantance ma’aikatan ƙananan hukumomi a faɗin ƙananan hukumomi 34, inda aka gano kusan ma’aikata 3,000 da aka samu matsaloli a bayanansu ko kuma suka kasa cika wasu sharuddan tantancewar.
