A baya-bayan nan dai mun ji yadda wasu jaruman masana'antar Kannywood da suka yi tsalle wuri guda suka barranta kansu daga tafiyar ƙungiyar Dauda Kahutu Rarara ta siyasa wayo Triple R, mun ji irin bayanan da ɗaya daga cikin Dattijan Kannywood Rabi'u Rikadawa ya yi, yayin ficewarsa daga tafiyar, wanda kalamai ne na rabuwar kai da rashin samun daidaito a kan tafiyar da ake yi a ƙungiyar. Haka nan mun jiyo Mansura Isah tsohuwar matar Sani Musa Danja wadda kalamanta suka yamutsa hazo bayan ficewarta daga ƙungiyar. Haka nan mun ji batutuwa marasa daɗin ji daga Dattijo Hamisu Iyantama a kan dai wannan tafiya ta Triple E, wanda shi ma tsohon darakta ne kuma tsohon mai shirya fina-finai ga shi kuma jarumi a masana'antar ta Kannywood.
Daga baya kwatsam! Sai kuma muka ji ita dai wannan tafiya ta yi sabbin kamu, inda ta gabatar da wasu dattijai da suka ƙunshi Alhaji Kabiru Maikaba da Al'amin Buhari da sauran dattijai da suka shiga cikin tafiyar. Bayan shi kuma akwai matasa da yawa waɗanda suka haɗa da: Garzali Miko da T.Y Shaba da Bilal Mustapha da Ɗan Hajiya da Furodusa Ɗan Hisba da Fati Shu'uma da kuma Fati KK wadda ta yi amai ta lashe, ta fita kuma yanzu ta dawo.
A taron ƙaddamar da sabbin mambobin ƙungiyar, jagoran tafiyar wato Dauda Kahutu Rarara ya bayyana manufofin ƙungiyar guda uku da suka haɗa da: 1. Zama tsakanin ƙungiyar da kuma gwamnati, tare da zama tsakiya tsakanin Triple R da kuma talaka. 2. Samar da wasu abubuwa a masana'antar Kannywood waɗanda ba a taɓa samar da su ba, musamman waɗanda za su bunƙasa masana'antar. 3. Taimakon kai da kai ('yan Kannywood).
A baya dai, bayan rikicin da ya ɓarke wanda ya sa wasu daga cikin Kannywood ɗin suka ɓalle daga tafiyar, an ji wani yunƙuri da ƙungiyar ta yi, inda ta biya wa wata 'yar Kannywood da take kwance asibiti ba lafiya naira miliyan 3m domin a yi mata aiki.
A taron ƙaddamar da sabbin mambobin dattijan Kannywood sun bayyana cewa: "Haƙiƙa Mun samu hujjojin yin jam'iyyar APC, kuma za mu zo da hujjojin nan ba da jimawa ba..."
Mu kuma muna nan mun zura na mujiya domin jin waɗannan hujjojin da wataƙila mu ma su sa mu samu hujjojin yin jam'iyyar ta APC.