Jami'an Tsaro Sun Yi Nasarar Kashe 'Yan Ta'adda 40 Har Da Kwamandojinsu

A yammacin ranar Lahadi ne, Kwamandan Ɓarayin daji Idi A Ba Su Aiki da ke yankin Bakori ya gayyaci ɗan'uwansa kwamanda Iliya Mai Rasha wanda ya addabi yankunan Tsafe da ke jihar Zamfara, ya kuma gayyaci wasu ɓarayin domin zuwa ɗaukar fansa a yankin Guga da ke ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

An tabbatar da cewa, sama da ɓarayi ɗari uku (300) ne waɗanda suke haye a saman babura da aƙalla sun wuce ɗari ɗauke da muggan makamai suka ɗunguma zuwa garin.

Mazauna yankin sun bayyana cewa, al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:30 na yamma na ranar Lahadi, inda suka shigo suka fara harbin kan mai uwa da wabi. Cikin nasara 'yan sa kan da ke cikin garin da kuma gamayyar 'yan C-watch suka yi yunƙurin daƙile harin, ta hanyar musayar wuta da suka ci gaba da yi da ɓarayin. Ana cikin wannan artabu kuma sai ga ƙarin dakarun sojoji daga Mabai da kuma jami'an 'Yan sanda daga Bakori, inda suka ci gaba da ragargazar ɓarayin a nan ƙauyen Dawan La'ila.

Bayan da wuta ta yi wuta, ɓarayin dajin sun ranta a na kare domin tseratar da rayuwarsu daga halaka, wanda a ƙoƙarin hakan suka gudu suka bar akwatina guda 2 da suke maƙare da alburusai. A wannan artabu an kashe ɓarayin daji sama da 40 daga cikinsu har da Kwamandan Tsafe wato Iliya Mairasha da wasu kwamandojin. An kuma ƙwace bindigu da mashina daga hannun ɓarayin.

Duk da haka, ɓarayin dajin sun yi wa jami'an tsaro ɓarna, inda suka halaka wani ɗan sa kai mai suna Babawo Ibrahim wanda shi har ma an yi masa sutura kamar yadda addini ya tanadar, an kuma kashe 'yan vigilante guda biyar. Allah ya gafarta masu, ya kawo mana ƙarshen wannan masifa.

Post a Comment

Previous Post Next Post